Najeriya bata nuna ba gun samar da 'yansandan jiha - IGP Idris

Najeriya bata nuna ba gun samar da 'yansandan jiha - IGP Idris

- Sufeto Janar na gaba daya na 'yansandan Najeriya, Ibrahim Idris ya bayyana cewa Najeriya bata gama nuna ba gun samar da 'yan sanda jiha a da ake maganganu akansa

- Idris ya bada cikarkiyar tabbas cewa tsarin tarayya na baki daya shi yafi cancanta lura da ababen da ke aukuwa a kasar na barazanar rashin zama lafiya.

Idris yayi wannan bayanin ne a cewar Legit.ng a jawabansa da yakeyiwa manema labarai a yayin wani taro na gwamnoni a Abuja a ranar Alhamis din da ta gabata.Idris ya nuna cewa tsarin 'yan sandan tarayya baki daya shine wanda yafi cancanta da kasarar Najeriya.

Mai magana da yawun 'yansanda Jimoh Moshood Ya nakaltoshi yana cewa yanada cikarkiyar tabbas cewa tsarin tarayya na baki daya shi yafi cancanta lura da ababen da ke aukuwa a kasar na barazanar rashin zama lafiya.

Najeriya bata nuna ba gun samar da 'yansandan jiha - IGP Idris
Najeriya bata nuna ba gun samar da 'yansandan jiha - IGP Idris

Masu kuruta a samar da tsarin 'yansandan jiha ya kamata su lura da yanayin cigaban kasar baki daya.

Gameda sa hannu a takardar tallafawa hukumar 'yan sanda, Idris ya nemi gwamnonin da suyi kokari gun tabbatar da an sa hannu akan abinda ya dace a majaalisa.

Ya nuna cewa yanada yakinin idan an zartar da takardar, hukumar ta 'yansanda zata ingantu a duk fadin kasar baki daya ta hanyar yin dukkanin abubuwan da kasa ke bukata daga garesu.

Ya kara da cewa yin hakan zai rage nauyi akan gwamnatin tarayya gun daukan nauyin hukumar da takeyi.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ba matsala ba ce - Okorocha

Idris ya bayyana a nakaltowar Legit.ng cewa hukumar na daga mafi karbar karancin albashi a kasahen duniya baki daya , tayanda majalisar dinkin duniya suka sanyasu karkashi kason 1:400.

A kalla hukumar 'yansanda sun debi ma'aikata 10,000 a wannan shekarar amma hakan bai kari hukumar da cikakken bukatarta ba na majalisar dinkin duniya (UN). Don cinma ka'idar ta Un na 1:400, hukumar 'yansandan na bukatar karin mutane 155,000 a karkashinsu.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel