Osinbajo ya umarci 'yan majalisa dasu gaggauta mayar da N135bn cikin kasafin kudin kasa na 2017

Osinbajo ya umarci 'yan majalisa dasu gaggauta mayar da N135bn cikin kasafin kudin kasa na 2017

- Mukaddasin shugaban ya aika sakon ne ta wasikar takarda wa 'yan majalisar

Mukaddasin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya nemi Majalisar zartarwa dasu gaggauta sa hannu gun tabbatarda an mayar da kudade N135 biliyan cikin kudaden kasafin kasa na shekarar 2017 don gudanar da ayyukan da aka tanada don su.

Sakon na mukaddasin shugaban ya kasance ne a wasikar takarda da ya aikawa yankin kasa na majalisar kasar Najeriya.

Ya aika makamanciyar wasikar a cewar Legit.ng wa majalisar Dattijai, amma shugaban majalisar Bukola Saraki, Amma bai karantawa yan majalisar ba.

Osinbajo ya umarci 'yan majalisa dasu gaggauta mayar da N135bn cikin kasafin kudin kasa na 2017
Osinbajo ya umarci 'yan majalisa dasu gaggauta mayar da N135bn cikin kasafin kudin kasa na 2017

A bayanan da wasikar ke dauke dashi, Za'a mayarda Naira biliyan N3.1bn wa ministairin Ayyuka da gine-gine, Biliyan N33bn wa ministiri na tafiye-tafiye; biliyan N14bn ofishin sakataren gwamnatin tarayya, biliyan N5 bn wa ofishin mai bada shawara na musamman wa harkar tsaro, biliyan N5bn wa ministirin kimiyya da fasaha, biliyanN3 bn wa ministirin tsaro, biliyan N3bn wa Birnin tarayya, biliyan N1bn ministirin kiwon lafiya.

KU KARANTA: Yan Najeriya suna nadaman zaben APC - Lamido

Majalisar Zartarwa ta yi jayayya da ministan Wuta,Ayyuka da gine-gine Babatunde Fashola sakamakon tsarin ayyukansa, amma daga baya sun sulhunta hakan a karshen lamari.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel