Gwamnatin Jihar Katsina Na harin sayan Motocin aikin noma 1000

Gwamnatin Jihar Katsina Na harin sayan Motocin aikin noma 1000

- Yunkurin ayyukan ya fara ne a wannan Alhamis 20 ga watan Yuli, ta hanyar farawa da motocin aikin gonan 225

- Shugaban kungiyar ta mamallaka motocin aikin gona (TOOAN) ya jinjinawa gwamnatin katsina a wannan kokarin nata datayi

Gwamnatin Jihar Katsina ta yawun mai bada shawara na musamman wa jihar Dr. Abba Abdullah, ta bayyana cewa tana haran motocin aikin noma guda 1000 don karfafa nomar zamani da bunkasa yawan amfanin gona a jihar.

Gwamnatin Jihar Katsina Na harin sayan Motocin aikin noma 1000
Gwamnatin Jihar Katsina Na harin sayan Motocin aikin noma 1000

Abdullah yayi jawaban ne a Jihar Katsina a jiya yayin kaddamar da wani taron zaburar da manoma komawa aikin noma, wanda yake gudanuwa da hadin guiwar kungiyar (Nigerian Incentive-based Risk Sharing System for Agricultural Lending NIRSAL), kamfanin Mahindra Tractor Manufacturing Company and Springfield Agro.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya yamutsa majalisar gudanarwar sa

Ya bayyana cewa yunkurin ayyukan ya fara ne a wannan Alhamis 20 ga watan Yuli, da motocin aikin(tractors) 225 wadanda zasu kai kudi kimanin Naira Biliyan biyu, kaso tamanin daga N1.6 biliyan din da aka nema daga bankuna don tallafi.

A jawabansa na karshe A nakaltowan Legit.ng ya nuna cewa tsawon lokacin biyan kudaden motocin ya kai watanni 48 daga lokacin kawosu. kuma tsare-tsare da tabbatuwar yuwuwar hakan daga lura da kungiyar mamallaka motocin aikin noma(Tractors Owners and Operators Association of Nigeria TOOAN) zasuyi don karfafawa.

Shugaban kungiyar ta TOOAN ya jinjinawa gwamnatin katsina a wannan kokarin nata datayi.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel