Gwamnatin tarayya ta raba tsarin karantarwar CRK da IRK a makarantun yara

Gwamnatin tarayya ta raba tsarin karantarwar CRK da IRK a makarantun yara

- Ministan Ilimi ya nuna akwai kokekoken iyaye gamada yawan karatun wa 'ya'yansu

- Yawan korafe korafe, musamman daga kungiyar kiristocin Najeriya (Christian Association of Nigeria CAN) an daga dalilin dayasa za'araba madojin biyu

Gwamnatin tarayya ta kasa ta umarci Hukumar Ilimi da ilmantarwa ta kasa (Nigerian Educational Research and Development Council NERDC) da ta raba tsakanin karantarwar addinin kiristanci da addinin musulinci.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayar da dokar a jiya a babban birnin tarayya Abuja a wani taron da kungiyar ilimi da ilmantarwa sukayi daga bangarorin kasar manya-manya guda shida.

Taran da kwamishinonin ilimi na dukkan jihohin tarayyan suka halarta ya kasance daga cikin kokarin tabbatarda kyautatuwan ilimi da akekira (Sustainable Development Goals 4 SDG4).

Ministan Ilimin ya nuna cewa Najeriya ta zabi karfafar wadannan manufofin guda 4 na SDGs, saboda sun kunshi; kyautatuwar bada bada ingantarcen ilimi da tafiyardashi a tsawon rayuwar karatu.

Adamu, a cewar Legit.ng wanda ministan cikingida ya wakilceshi Farfesa Anthony Anwukah, yace raba tsarin karantarwar addinan guda biyu abune mai matukar mahimmanci sakamakon yawan korafe korafe, musamman daga kungiyar kiristocin Najeriya (Christian Association of Nigeria CAN).

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya yamutsa majalisar gudanarwar sa

Ya kara da cewa raunin da karatun ya samu ba ta sanadin wannan gwamnatin bane, amma na gwamnatin da ta gabata a yunkurinta an takaita yawan karaturtukan da yaran makaranta keyi.

A wani bayanan nasa da Legit.ng ta nakalto ya nuna akwai tsokaci da gunaguni gameda hada madodin addinan guda biyu da akayi, da kuma kokekoken iyaye gamada yawan karatun wa 'ya'yansu.

Ya kara da cewa gwamnatin kasa na sane da dukkan ire-iren abubuwan nan da kuma kokarin da takeyi gun cinma burin ajendar ilimi ta 2030, wacca ta kunshi magance matsalar dakeda alaka da karaturtukan yara yan makaranta.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel