Dalilan da sukasa naki yarda da tayawar da gwamnati tayi na bani biyafara – Nnamdi Kanu

Dalilan da sukasa naki yarda da tayawar da gwamnati tayi na bani biyafara – Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar kokarin tabbatar da Biyafara (Indigenous People of Biafra,IPOB) Nnamdi Kanu ya bayyanar da cewa Gwamnatin Najeriya ta basa damar tabbatar da Biyafara amma yaki karban tallatawar.

A jawabanda da Legit.ng ta nakalto na Ranar Laraba, kanu ya bayyana cewa an tallata masa basa damar ne a yayin da yake cikin kurkuku, amma yaki hakan skamakon Jihohin da aka basa guda biyar ne kadai.

Dalilan da sukasa naki yarda da tayawar da gwamnati tayi na Bani biyafara – Nnamdi Kanu
Dalilan da sukasa naki yarda da tayawar da gwamnati tayi na Bani biyafara – Nnamdi Kanu

Ya kara da cewa a tareda Jihohin guda biyar da akayi masa alkawarin akwai,har ila 'iyau rijiyar man fetur da katafaren gini a Dubai aka masa alkawari, duk anyi hakan ne da manufar ya bar Ra'ayinsa na tabbatar da biyafara.

A wasu daga bayanan nasa ya nuna cewa sun baji jihohi biyar a yayin da nake fursina, ni kuma na nemi a kara min da Benuwe da Rivers.Ya kara da cewa Biyafara na nan tafe kuma babu abinda zai hana hakan yiwuwa.

KU KARANTA: Ku dauke Rundunar ku daga Jihar Bayelsa - 'Yan Majalisa sun gargadi Sojoji

A taron da akayi na Hadin kan Inyamiran farar hula,wanda Farfesa obasi igwe ya jagoranta, kanu ya kushe ragowar inyamiran da suka ki basa goyon baya a yunkurinsa na tabbatar da Biyafara.

A karshe ya nuna cewa inyamuran da suka ja kujerar naki ba karamin hasara suke jawowa kansu da tabbatuwar Biyafara ba.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel