Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umarni a saki wani Gwamna da aka yankewa dauri

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umarni a saki wani Gwamna da aka yankewa dauri

- Kotu ta bada umarni a saki tsohon Gwamnan Jihar Adamawa

- Alkalin Kotun daukaka kara ya nemi ka da a rufe Bala Ngillari

- An dai zargi tsohon Gwamnan Adamwan da laifuffuka har 19

Kotun daukaka kara da ke Jihar Adamawa ta bada umarni a saki tsohon Gwamnan Jihar Mista James Bala Ngillari bayan da fari wani Alkali ya nemi a rufe sa a gidan Yari.

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umarni a saki wani Gwamna da aka yankewa dauri

Hoton tsohon Gwamna Bala Ngilari daga yanar gizo

Ana zargin tsohon Gwamna Bala Ngilari da satar wasu kudi a lokacin da ya rike mulkin Jihar Adamawa bayan an tsige Gwamna Murtala Nyako. Har yanzu dai Hukumar EFCC ba ta ce komai ba game da batun.

KU KARANTA: Ashe yawon talla bai da aibu?

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umarni a saki wani Gwamna da aka yankewa dauri

Kotu ta wanke James Bala Ngilari

Hakan ya sa Alkali Nathan Musa na babban Kotun Tarayya ya nemi a daure tsohon Gwamnan bayan ya same sa da rashin gaskiya wanda daga baya aka karbi belin sa a kan kudi Naira Miliyan guda. Yanzu dai Kotu ta wanke tsohon Gwamnan na Adamawa kal.

Shugaban kwamitin da ke kula da harkar shigo da kaya cikin Najeriya a Majalisar Dattawa Sanata Hope Uzodinma ya koka da yadda ake shigo da kaya ta barauniyar hanya cikin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Matan Jam'iyyar PDP sun koka da lamarin kasa

Source: Legit

Mailfire view pixel