Rashin lafiyar Buhari na jinkirtar da Babban taron APC -Yari

Rashin lafiyar Buhari na jinkirtar da Babban taron APC -Yari

- Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz YariYa alakanta, tareda sababantar da jinkirin babban taronsu na Jam'iyyar APC da Rashin Lafiyar shugaba Muhammadu Buhari.

- Yari ya nuna cewa taron ya kasa yuwuwa ne sakamakon rashin kasantuwar Shugaba Muhammadu buhari a kasar

Abdullahin yayi wadannan jawaban ne a ranar Laraban da ta gabata a yayin wani taro na manema labarai tareda Bolaji Abdullahi,mai magana da yaun Jam'iyyar ta APC a sakateriyarsu a Birnin Abuja.

Ya kara dacewa mun dade a kan wannan lamari don rashin kasantuwar shugaba a kasa a matsayinsa na jagora wannan taro mai girma da za'ayi.

Mun dade muna sanya lokuta don taron kuma muna dage su saboda samun cikas gurin tabbashin dawowar shugaban.

Rashin lafiyar Buhari na jinkirtar da Babban taron APC -Yari
Rashin lafiyar Buhari na jinkirtar da Babban taron APC -Yari

Yayi ya nuna cewa manyan Jam'iyyar zasu yi ganawar musamman da Mukaddasin kasar Yemi Osinbajo a kan wannan lamarin.

Yari ya tabbatar da taron a cewar Legit.ng zai auku a 29 ga watan Yuli wanda zai kunshi dukkanin bangarorin kasar baki daya.

KU KARANTA: Osinbajo ya yi Magana kan rikicin Kudancin Kaduna

Ya Nuna cewa zaben gefe sanatan da akayi na nasarar Ademola Adeleke a jam'iyyar PDP gargadi ne gameda tashi tsaye da ya kamata yan Jam'iyyar APC suyi.

Sun tattauna gameda zaben Osun tareda sanin cewa PDP batada damar lashe zaben , amma magudi da murda-murda sun haifar da hakan. don magance maimaituwar hakan ya kamata mu tashi tsaye akan lamurran tararrakin mu.

Kasancewar Muna zamanin dimokradiyya ne, kuma a bisa adalci da manuniya ta nuna, dan'uwan dan takaran dan APC ne, kuma karkashinsa shima ya cigaba amma ga irin abin da ya auku nan. saboda haka bazamu bar maimaituwar hakan ba a gaba.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel