Wani kudirin dokar yafe wa barayin gwamnati ya jawo cece-kuce

Wani kudirin dokar yafe wa barayin gwamnati ya jawo cece-kuce

- Kudurin doka da zai yafe wa batayin gwamnati ya jawo cece kuce

- Ana duba yiwuwar yafe wa barayi muddin suka dawo da kudi

- Wasu na ganin hakan daidai yake da azo a ci bulus

Kudurin da aka fi sani da, "kudurin yafewa barayin gwamnati", ya Samu gabatarwa ne a majalisan dokoki, daga, dan majalisa, Linus Okorie dake wakiltar Ohaukwu/Ebonyi state federal constituency na jam'iyar PDP.

A nashi bangaren yace "kudurin Zai baiwa wananda suka mallaki arziki ta haramtacciyar hanya, don sun bayyanar da nawa suka sata, sannan Kuma, su biya hará ji tare da tillasta másu Don sa hannun Jari a cikin kasa. Sai Kuma a yafe masu in Sunyi hakan, tareda karesu daga tuhuma."

Wani kudirin dokar yafe wa barayin gwamnati ya jawo cece-kuce
Wani kudirin dokar yafe wa barayin gwamnati ya jawo cece-kuce

Wannan kudurin ya jawo zazzafar adawa a baynar jama'a. Don mafi yawancin jama'a na ganin cewa, wannan wata sabon salo ne na yunkurin yin zagon kasa da gwamnati ke yi ga cin hanci da rashawa, da Kuma badakala da dukiyar alumomin najeiya.

DUBA WANNAN: Atiku ya caccakin jam'iyyarsa ta APC

Cikakken bayani Gameda kudurin:

Kudurin ya kwaikwayi wani kudurin "economic amnesty" na "section 4", Wanda ya bayyana cewa, gwamnati za ta caji kashi talatin (30) na haráji, da kuma wani kashi (25) na irin wanan hará ji don rabawa tsakanin matakai Guda uku na gwamnati,

Wato; masu guadañarwa (executives), masu Kafa dokoi( legislative) da Kuma masu hukunta wanda suka karya dokoki ( judiciary). Sanan kuma za a tilasta don sa hannun jari na kashi talatin na dukiyar da aka sata a harkar noma, Sauran kuma za a sa hannun jari a wash fanni na kasa. Bayan tarar kashi 30 da kuma kashi 25, kudurin ya kubutar da dukiyar daga biyan ko wane irin haráji a gaba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel