Buhari zai dawo daga Landan a ranar 27 ga watan Yuli – Sahara Reporters

Buhari zai dawo daga Landan a ranar 27 ga watan Yuli – Sahara Reporters

Sahara Reporters ta bayyana cewa na kewaye da fadar shugaban kasa zasu dawo da shugaba Buhari kasar a watan Yuli.

Shahararriyar jaridar nan ta wato Sahara Reporters ta fitar da wani sabon rahoto kan yadda na kewaye da fadar shugaban kasa ke kokarin dawo da shugaba Muhammadu Buhari gida Najeriya daga London inda ya ke jinya.

Sahara Reporters ta rawaito cewa, makusanta shugaba Buhari sun bai wa uwargidar shugaban kasar cikakkiyar damar ganin mijin nata a yanzu sannan kuma sun saka ranar da shugaban kasar zai dawo gida Najeriya a matsayin ranar 27 ga watan Yuli, 2017.

Zuwa yanzu dai Shugaba Buhari ya kwashe tsawon kwanaki 73 a birnin Landan, inda ya ke jinyar wata lalura da ba a bayyanawa jama’a cikakkiyar bayani a kan ta ba.

KU KARANTA KUMA: Allah yayi wa dan majalisan dokoki na jihar Lagas rasuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar gida Najeriya zuwa birnin London a ranar 7 ga watan Mayu, 2017.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna son bamu shawara ko bamu labarai tuntube me a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel