Nigerian news All categories All tags
Yadda El-Rufai ya ki Buhari a 2010 amma yake yaba masa a 2017

Yadda El-Rufai ya ki Buhari a 2010 amma yake yaba masa a 2017

- Gwamnan jihar Kaduna ya bukaci shugaba Buhari ya bar siyasa a 2010

- Tsohon ministan na birnin tarayya ya bayyana Buhari a matsayin dan takara da bazai moru ba

- Amma a yanzu El-Rufai ya zamo daya daga cikin manyan magoya bayan Buhari

Sabanin sabon wakokin sa na yabo ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, a shekarar 2010 gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana Janar din waccen lokaci Muhammadu Buhari a matsayin dan takara da ba zai iya tabuka komai ba.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara a shafukan zumunta, Reno Omokri ne ya bayyana wasu jaridu a shafin san a Facebook inda El-Rufai ke sukar tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayinda ya bayyana su a matsayin yan takara da suka tashi daga aiki.

KU KARANTA KUMA: Ta sayar da jaririnta akan N700,000, an bata rabin buhun shinkafa a maimakon Kudin

A cewar jaridar Sun na ranar 20 ga watan Satumba, 201o, El-Rufai ya bukaci Babangida da Buhari da su janye takarar shugabancin kasa a 2011.

A halin yanzu, Legit.ng ta rahoto cewa tsohon kakkakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya bayyana shugaban kasa mai ci a matsayin ‘kuskure’.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel