Dan wasan Najeriya, Kelechi Iheanacho ya tashi daga Man City zuwa Leicester City

Dan wasan Najeriya, Kelechi Iheanacho ya tashi daga Man City zuwa Leicester City

- Matashin dan wasa Kelechi Iheanacho ya koma Leicester

- Kungiyar Manchester City ta raba gari da dan wasan Najeriya

Fitaccen dan wasan Najeriya, Kelechi Iheanacho na gab da yin sauya yin sheka daga kungiyar Machester City zuwa kungiyar Leicester City, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Iheanacho zai tashi daga Man City ne bayan mai horar da kungiyar, Pep Guardiola ya fifita Gabriel Jesus da Sergio Aguero fiye da shi.

KU KARANTA: Anyi gangamin fara yi ma ɗan majalisa Abdulmuminu Jibrin kiranye a garin Dakatsalle

Da fari dai kungiyoyi daban daban na cikin wadanda suke neman zawarcin Iheanacho, kungiyoyin sun hada da Everton da Westham, amma daga karshe, Iheanacho ya fi nuna gamsuwa da Leicester City.

Dan wasan Najeriya, Kelechi Iheanacho ya tashi daga Man City zuwa Leicester City
Kelechi Iheanacho

Idan Iheanacho ya kammala sauyin shekar zuwa Leicester , zai hade da sauran yan wasan Super Eagles Ahmed Musa da Wilfried Ndidi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel