Nigerian news All categories All tags
El-Rufai: Gwamnan jihar Kaduna ko Baban yara? Kalli haɗuwarsa da wasu yara (HOTUNA)

El-Rufai: Gwamnan jihar Kaduna ko Baban yara? Kalli haɗuwarsa da wasu yara (HOTUNA)

- Hotunann El-Rufai da kananan yara sun sake bayyana

- Gwamnan jihar Kaduna ya tarbi wasu baki da yayi kananan yara a ofishinsa

Wasu hotunan gwamnan jihar Kaduna sun watsu a shafukan yanar gizo, inda aka gansa yana karrama wasu kananan yara yayin da suka kawo masa ziyara a ofishinsa.

Wani ma’bocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Adamu Hayatuddeen ne ya daura hotunan, inda yace babban burin yaran shine su gana da gwamnan na jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.

KU KARANTA: Ke Duniya: Matashi ya hallaka abokinsa ta hanyar farke masa ciki don ya kwashi kayan cikinsa (HOTUNA)

Legit.ng ta ruwaito Hayatuddeen yana fadin sau biyu kenan yaran suna zuwa domin ganin gwamnan a gida amma basu same shi ba, sai a wannan zuwan ne suka samu daman ganins a ofishinsa.

El-Rufai: Gwamnan jihar Kaduna ko Baban yara? Kalli yadda haɗuwarsa da wasu yara (HOTUNA)

El-Rufai tare da Ishaq da Hayatu

“Ishaq da Hayatuddeen sun samu ganin gwamna Nasir El-Rufai a ofishinsa, gwamnan ya basu lokacinsa har ma ya daure musu igiyar takalmi. Yaran nan ba zasu taba mantanwa da yadda gwamnan ya tarairaye su ba” inji Hayatuddeen.

El-Rufai: Gwamnan jihar Kaduna ko Baban yara? Kalli yadda haɗuwarsa da wasu yara (HOTUNA)

El-Rufai tare da yaran

A baya ma an taba ganin hotunan gwamnan tare da kananan yayansu suna wasa a dakinsa, yana yi musu macululu.

El-Rufai: Gwamnan jihar Kaduna ko Baban yara? Kalli yadda haɗuwarsa da wasu yara (HOTUNA)

Gwamna tare da yaran

El-Rufai: Gwamnan jihar Kaduna ko Baban yara? Kalli yadda haɗuwarsa da wasu yara (HOTUNA)

El-Rufai da yayansa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka iya taimaka ma Buhari da kodarka idan ya bukata?

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel