Matasan PDP sun yi kira da a daina yada jita-jita akan hukuncin Kotun Koli

Matasan PDP sun yi kira da a daina yada jita-jita akan hukuncin Kotun Koli

- Wasu matasan jam’iyyar PDP sun nuna damuwa kan yadda ake yada karya a kan hukuncin da Kotun Koli za ta zartar kan rikicin shugabanci a jam'iyyar

- Matasan sun bukaci sanata Ali Modu Sheriff da ya tsawatarwa magoya bayansa domin su guji yada farfaganda

- Kungiyar ta ce amfani da kafafen sadarwa na zamani kan hukuncin da ba a yi ba zai iya tarwatsa kima da nagartar fannin shari'a

Kungiyar Jakadun samar da canji da hadin kai a Najeriya ta jam'iyyar PDP wato (PDP Youths Ambassadors for change and Unity in Nigeria) ta nuna matukar damuwa kan yadda ake yada karya a kafafen sadarwa na zamani musamman daga bangaren sanata Ali Modu Sheriff kan hukuncin da Kotun Koli za ta zartar kan rikita-rikitar shugabanci a jam'iyyar.

Kungiyar ta bukaci shugaban bangare na PDP, sanata Ali Modu Sheriff da ya tsawatarwa magoya bayansa domin su guji yada farfaganda da jita- jitar da babu kamshin gaskiya a ciki a shafukan sada zumunta.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, sakataren kungiyar na kasa kwamred Yusuf Abubakar ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Sakwatto tare da kara bayyana cewar ya zama wajibi shugabannin PDP a bangaren Sheriff su dakatar da wasa da hukuncin da kotu za ta yanke.

Matasan PDP sun yi kira da a daina yada jita-jita akan hukuncin Kotun Koli

Wadata plaza, babban ofishin jam'iyyar PDP da ke Abuja

Ya ce kuskure ne matuka wasa da kima da martabar sashen shari'a ta hanyar amfani da kafafen sadarwa na zamani a na yada hukuncin da ba a riga aka yi ba wanda hakan zai iya tarwatsa kima da nagartar fannin shari'a.

KU KARANTA: Muna nan a kan bakarmu na kowani dan Kabilar Igbo ya koma ‘yankinsa – Kungiyar matasan Arewa

Abubakar ya ce: "Mun yi Allah wadai da dabarar da suka fito da ita da farko cewar Kotun Koli ta tabbatar da sanata Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban PDP a yanzu kuma suna amfani da wasu hanyoyi na karya na kokarin jefa alkalai masu mutunci da dattako kan abin da ba haka yake ba kan hukuncin wanda ba gaskiya ba ne."

Ya ci gaba da cewa:"Har yanzu Kotun Koli ba ta sanya ranar yanke hukunci kan takaddamar shugabancin PDP ba kuma ba ta bayyanawa wadanda lamarin ya shafa ranar da za a yi zaman zartar da hukuncin ba. Don haka bisa ga yadda suke tafiyar da lamurra za a fahimci cewar yunkurinsu shine su haifar da matsala da illa ga sashen shari'a kamar yadda suka haifar wa jam'iyyar mu ta PDP."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani jami'in jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa 2019

Source: Legit

Mailfire view pixel