Akwai bukatar sake bitar farashin kujerun aikin Hajji a Najeriya

Akwai bukatar sake bitar farashin kujerun aikin Hajji a Najeriya

- ‘Yan Najeriya da dama na korafi game da farashin kujerar aikin hajjin bana inda suka bukaci cewa akwai bukatar sake bitar farashin

- Ambassada Usman ya bayyana cewa kudin da yakamata Alhazai su biya shine naira miliyan 1.2, maimakon naira miliyan 1.5.

- Usman ya danganta farashin kujerar aikin hajjin cewa sakaci ne daga bangaren gwamnatin tarayya

Yayin da ‘yan Najeriya musamman maniyyata aikin hajjin bana ke ci korafi game da farashin kujerar aikin hajji da hukumar alhazan kasar ta kayyade, na fiye da naira miliyan 1.5 ga kowane Alhaji.

Masana harkokin aikin Hajji da Umara a kasar na bayyana bukatar dake ga gwamnati ta sake bitar farashin kujerun aikin hajjin da nufin saukakawa maniyyatan na bana.

Ambassada Usman Darma, mataimakin shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Kano kuma shugaban kamfanin shirya zirga zirga na Darma Air ya danganta lamarin da sakaci daga bangaren gwamnatin tarayya.

Akwai bukatar sake bitar farashin kujerun aikin Hajji a Najeriya

Masallacin Ka'aba

KU KARANTA: Abdulmuminu Jibrin ya yi wa mutanen mazabar shi tara ta arziki (Hotuna)

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Ambassada Usman ya ce sunyi nazari kan yadda kudaden zuwa aikin hajji zasu kasance, inda ya ce tun daga kan kudin jirgi zuwa masauki da guzuri baki daya, kudin da yakamat Alhazai su biya shine naira miliyan 1.2, maimakon naira miliyan 1.5.

A cewar Ambasada rashin saka ido ne ya haifar da wannan matsala ta hauhawar farashin kujerar aikin hajjin bana, inda yace ya kamata gwamnati ta rika tabbatar da cewa hukumar da ke da alhakin wannan aiki tana yin aikin da yakamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel