Sarki Sanusi ya kori sakataren sa daga aiki a bisa zargin yi masa zagon kasa

Sarki Sanusi ya kori sakataren sa daga aiki a bisa zargin yi masa zagon kasa

- Muhammadu Sanusi na II ya kori sakataren masarautar Kano

- An kori sakataren ne bisa zargin cewa shi ne sillar duk wasu muggan labarai da ke fitowa a shafukan yada labarai game da sarkin

Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya kori sakataren masarautar Kano, Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot daga aiki akan zargin yi wa masa zagon kasa.

Legit.ng ta samu labarin cewa wata majiya daga masarautar ta bayyana wa jaridar Leadership cewa korarren sakataren shi ne sillar duk wasu muggan labarai da ke fitowa a shafukan yada labarai game da sarkin.

KU KARANTA KUMA: Ashe Shugaba Jonathan ne ya dagargaza tattalin arzikin kasar nan

Sarki Sanusi ya kori sakataren sa daga aiki a bisa zargin yi masa zagon kasa

Sarki Sanusi ya kori sakataren sa daga aiki a bisa zargin yi masa zagon kasa

A cewar majiyar wanda ya nemi a sirrinta sunan sa, korarren sakataren shi ya fitar da takardun bayanan kashe kashen kudaden masarautar ga ‘yan jarida, wanda a sakamakon haka ya haddasa rikicin da ke tsakanin sarki Sanusi da gwamnatin Kano da majalisar jaha.

Wata majiyar daban da ya yi aiki a karkashin Isa Pilot ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce ba boyayyen abu bane a fadar kiyayyar da tsohon sakataren ke yi wa Sarki Sanusi.

KU KARANTA KUMA: Tsarin TSA na Buhari bai da amfani Inji wani tsohon Gwamnan CBN

Ya ce rikicin da ya barke tsakanin Sarkin da gwamnatin Kano shi ne babban abun da ya fallasa sakataren.

Rahotanni sun bayyana cewa kanin Sarki Sanusi, Mustapha Lamido Sanusi wanda aka nada a matsayin Falakin Kano shi ne ya maye gurbin sakataren.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na Legit.ng wanda a ciki ne Sarkin Kano Sanusi Lamido ya soki tsarin gwamnatin kasar

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel