Manyan jaruman Kannywood sun taka rawar gani a fim din SULTANA

Manyan jaruman Kannywood sun taka rawar gani a fim din SULTANA

- Fim din Sultana na kamfanin shirya fina-finan Hausa ya tara dandazon jiga jigan jaruman Kannywood a guri

- Jama’a sun iya gane haka ne a tirelan fim din wanda kamfanin ya saki ta shafin sa na Instagram

- Nafisa Abdullahi ta taka rawar gani matuka a cikin fim din

Fim din Sultana na kamfanin Abdul Amart Maikwashewa fim ne da ya tara dandazon jiga jigan jaruman Kannywood a guri daya, inda kowannen su kuma ya kure bajintar sa.

Jama’a sun iya gane haka ne a tirelan fim din wanda kamfanin ya saki ta shafin sa na Instagram.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Biyafara ta mika ‘Sa’ Mai suna ‘Buhari’ ga shugabansu (HOTUNA)

Manyan jaruman Kannywood sun taka rawar gani a fim din SULTANA
Manyan jaruman Kannywood sun taka rawar gani a fim din SULTANA

Masoya fina finan hausa sun yaba musamman da rawar da Nafisa Abdullahi ta taka a cikin fim din, inda suka ce sun kosa da jiran fim din ya fito.

Manyan jaruman Kannywood sun taka rawar gani a fim din SULTANA

Wadanda suka fito a Sultana sun hada da, Sarki Ali Nuhu, Nafeesa Abdullahi, Adam A. Zango, Hauwa Maina, Wash Waziri da sauransu.

Nazir Alkanawy shi ya rubuta labari, Nura M, Inuwa ya dauki nauyi, yayin da Adam A. Zango ya bada umarni.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel