Ana cacar baki tsakanin Jonathan da El-Rufai

Ana cacar baki tsakanin Jonathan da El-Rufai

– Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya maidawa Gwamna El-Rufai martani

– Gwamna El-Rufai babban makaryaci ne Inji tsohon Shugaban kasar

– El-Rufai yace Jonathan ya rabawa Jihohin PDP wasu kudi a lokacin mulkin sa

Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya kira Gwamnan Kaduna babban makaryaci

Mai magana da yawun Jonathan yace Gwamnan yak ware da karya.

El-Rufai yace tsohon Shugaban kasar yayi son kai lokacin yana mulki.

Ana cacar baki tsakanin Jonathan da El-Rufai

Rikicin El-Rufai da tsohon Shugaba Jonathan ya kara kamari

Rikicin Gwaman Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da Tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya kara kamari bayan El-Rufai yace tsohon Shugaban kasar yayi son kai lokacin yana mulki inda ya fifita Gwamnonin PDP da su ke tare.

KU KARANTA: An karrama wasu Gwamnoni guda 6

Ana cacar baki tsakanin Jonathan da El-Rufai

Jonathan yayi son kai lokacin yana mulki-El-Rufai

El-Rufa’i yace akwai wasu Biliyoyi da Jonathan ya ware ga Jihohin PDP inda ya hana sauran Gwamnonin Jam’iyyun adawa har ma da Gwamnonin PDP da ba su ga maciji. Ikechukwu Eze mai magana da bakin Jonathan yace karya Gwamnan yake yi domin ka’ida aka bi wajen rabon.

Kun ji akwai wata badakalar da aka buga wajen saida rijiyar man kasar nan na Malabu a lokacin Jonathan. Ministan da ake tuhuma Adoke ya bayyanawa Kotu cewa duk abin da yayi a wancan lokacin shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya sa shi ya kuma amice.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Osinbajo da Obasanjo a wajen wata lacca

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel