Kungiyar Chelsea ta suburbude kofin Firimiyar Ingila

Kungiyar Chelsea ta suburbude kofin Firimiyar Ingila

- An tabbatar wa Chelsea kambun Firimiyar Ingila ta bana, bayan ƙwallon da Michy Batshuayi ya ci a ƙarshe-ƙarshe, ta bai wa kulob ɗin nasarar da yake buƙata don ɗaukar gasar a West Brom.

- Da farko dai kamar za a tilasta wa ƙungiyar ta Antonio Conte jinkirin lashe gasar Firimiya, don kuwa masu karɓar baƙuncinsu sun yi ta daƙile yunƙurinsu.

Sai dai rawa ta sauya, inda Chelsea ta lashe gasar ana saura minti takwas lokacin da Batshuayi ya shauɗa ƙwallon da ta wuce ta saman Ben Foster bayan ya yi canji ya shigo.

Legit.ng ta samu labarin gagarumar murna da tsalle-tsalle sun kaure a tsakanin magoya bayan Chelsea, bayan lafari ya busa tashi, inda 'yan wasan Antonio Conte suka riƙa cilla shi sama suna cafewa.

Kocin ɗan ƙasar Italiya ka iya sa ran yin koyi da bajintar takwaransa Carlo Ancelotti ta shekara 2010, wanda ya lashe gasar Firimiya da kuma Kofin FA.

Kungiyar Chelsea ta suburbude kofin Firimiyar Ingila
Kungiyar Chelsea ta suburbude kofin Firimiyar Ingila

KU KARANTA: Har yanzu ba'a aikawa Osinbajo da kasafin kudi ba

A ranar 27 ga watan Mayu ne Chelsea za ta kara da a wasan ƙarshe na cin Kofin FA da Arsenal a filin wasa na Wembley.

Chelsea dai ta cancanci nasarar da ta samu, sakamakon ƙasaitaccen aikin da Antonio Conte da kuma ayarin 'yan wasansa suka yi.

Sun yi namijin ƙoƙari don samun galaba a kan West Brom wadda ta nuna da gaske ta shiga fagen karawar.

Rashin nasarar da Chelsea ta yi a gida a hannun Liverpool da Arsenal a watan Satumba sun zama tarihi, gami da cin ba-zata da Crystal Palace ta yi mata a Stamford Bridge da kuma koma-bayan da ta samu a hannun Manchester United.

Kai hatta lokacin da ta fito babu cikakken ƙarfi, Chelsea ta nuna kanta a matsayin ƙungiya mafi ƙarfi da ta haɗa komai a gasar Firimiya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel