Mun bani: Cutar Ebola ta dawo Afrika

Mun bani: Cutar Ebola ta dawo Afrika

– Cutar nan Ebola ta dawo cikin Nahiyar Afrika

– Yanzu haka cutar ta kashe Jama’a a kasar Congo

– Ebola dai tana kisa cikin lokacin kan-kani

Cutar nan da ta kashe Jama’a ta kara dawowa Afrika.

Dama kwanakin bayan WHO tace babu makawa sai cutar Ebola ta dawo.

Dole Jama’a su yi hattara domin cutar na kisa.

Mun bani: Cutar Ebola ta dawo Afrika
Cutar Ebola mai kisa ta dawo Afrika

Tun a kwanakin baya Legit.ng ta bayyana maku cewa Cutar nan ta Ebola na shirin dawawo kasashen Duniya. Sai dai ba a san a ina cutar za ta barke ba kamar yadda Hukumar kula da lafiya ta Duniya WHO ta fada.

KU KARANTA: An yi musanyar 'Yan ta'adda da Matan Chibok

Mun bani: Cutar Ebola ta dawo Afrika
Cutar Ebola ta hallaka Jama'a a Congo

Ga shi dai yanzu cutar ta barke a Kasar Congo inda har mutane akalla 3 sun bakunci lahira. Ministan lafiya na kasar ya tabbatar da wannan bayan an samu Jama’a da dama na fama da zazzabi.

Shekaru 3 da su ka wuce cutar ta hallaka mutane kusan 50 a annobar da ta barke. Gaba daya dai a shekarar 2013 annobar tayi barna a Afrika musamman irin su kasar Liberia, Guinea, da Sierra Leone inda aka rasa mutane sama da 11,000.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shugaban Najeriya bai da lafiya [Bidiyo]

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel