Gasar Nahiyar Turai: Juventus za ta kara da Real Madrid a wasan karshe

Gasar Nahiyar Turai: Juventus za ta kara da Real Madrid a wasan karshe

– Wannan karo ma dai Kungiyar Real Madrid karasa zagayen karshe a gasar Champions League

– Real Madrid na iya kafa tarihin da ba a taba ba

– Babu kungiyar da ta taba cin kofin sau 2 a jere

Duk da Real Madrid ta sha kashi a hannun makwabtan ta Atletico Madrid ta isa wasan karshe.

Watakila Real Madrid din tayi abin da ba a taba yi ba bana.

A shekarar 98 dai Real Madrid ta doke Juventus a wasan karshe.

Gasar Nahiyar Turai: Juventus za ta kara da Real Madrid a wasan karshe
Real Madrid ta doke Atletico Madrid

An dauki shekaru da dama babu Kungiyar Kasar Italiya da ta dauki kofin UEFA Champions League na zakarun Nahiyar Turai tun bayan AC Milan. A wata fafatawa da aka yi a 1998 dai Real Madrid ta doke Juventus a wasan karshe.

KU KARANTA: UCL: Juventus ta doke Kungiyar Monaco

Gasar Nahiyar Turai: Juventus za ta kara da Real Madrid a wasan karshe
Gasar Nahiyar Turai: Real Madrid ta isa wasan karshe

Bara dai Real Madrid din ce ta dauki kofin ko wannan karo za ta bar tarihi tayi abin da ya gagari kowa na daukar kofin sau 2 a jere. Atletico ta doke Real Madrid a wasan da ci 2- 1, sai dai wannan bai yi tasiri ba don Real Madrid din tayi nasarar 3-0 a wasan farko.

Jiya kun ji cewa Juventus ta isa zagayen karshe a gasar UEFA Champions League na zakarun Nahiyar Turai bayan ta doke Monaco ta Faransa da ci 2-1. A zagayen farko Juventus tayi nasara da ci biyu da nema.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Manyan labaran wannan mako

Source: Legit

Online view pixel