JAMB zatayi amfani da Hukumar EFCC, ICPC, DSS gurin gudanar da jarrabawarta a bana

JAMB zatayi amfani da Hukumar EFCC, ICPC, DSS gurin gudanar da jarrabawarta a bana

- Hukumar ta JAMB zata sanya na'urar daukan hotuna da bidiyo guda 624 a guraren jarrabawowinsu a fadin kasa baki daya

- Farfesa Ishaq Oloyede ya nuna daga yanzu jarrabawar UTME bazata zama gurin cin kasuwar cin hanci da rashawa ba kamar yarda akeyi a baya

Majibinta lamarin Joint Admission and Matriculation Board (JAMB), sun bada sanarwar cewa zasuyi amfani da ma'aikata daga kungiyar yansanda,Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC da sauran hukumomin fada da rashin gaskiya a guraren jarrabawarta mai gabatowa Unified Tertiary Matriculation Examination (UMTE).

Hukumar ta kara da cewa zasu sanya na'urar daukan hotuna da bidiyo guda 624 a guraren jarrabawowinsu a fadin kasa baki daya a ranar Asabar tareda amfani da taimakon taimakon hukumomin Nigerian Security and Civil Defence Corps, NSCDC, the Department of State Services, DSS and special security forces don tabbatuwar kyautatar abinda aka sa gaba.

Maga takardar hukumar JAMB, Prof. Is-haq Oloyede a bayaninsa wa manema labarai a Abuja ya tabbatar da cewa kowanna gurin jarrabawa zai sami mai lura ,mai sa ido,mai tabbatarwa da kuma jami'an tsaro guda uku.

Ya kara a fadar Legit.ng da cewa, “kowacca jiha zata zamana tana karkashin kulawar shugaban babbar makaranta, Jami'a ko kwaleji."

KU KARANTA: Sakin yan matan Chibok abin farin ciki ne - Gwamnatin Amurka

”Ya zartar da cewa daga yanzu Jarrabawar UTME bazata zama gurin cin kasuwar cin hanci da rashawa ba kamar yarda akeyi a baya.

“A daga cikin tsare-tsaren Hukumar jarrabawar a kwai tabbatartun matakai da hukunce-hukunce ga wadanda aka kama da satar jarabawa, sauya sakamakon jarrabawa da sauran dangin laifurfukan da ke iya aukuwa.

“A yanzu haka mun kama dayawa daga masu birkita mana lamarin jarrabawa ta hanyar yanar gizo-gizo da na'urar kwamputa, kuma munyi hakan ne don tauna tsakuwa saboda aya taji tsoro.''

Maga takardaj din ya gargadi masu zana jarrabawa da kada su biyewa yan damfara da ke iya yi musu alkawurran karya ko sakwannin neman bayanai daga garesu gun kyautatuwar jarrabawarsu da nufin karbar kudi daga garesu.

Ku biyomu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya sun fadi na bakinsu a Komawar Buhari Landan.

Source: Legit

Online view pixel