Dogarin Marigayi Abacha ya kafa sabuwar Jam’iyya

Dogarin Marigayi Abacha ya kafa sabuwar Jam’iyya

– Dogarin Abacha, Al-Mustapha ya kafa sabuwar Jam’iyya

– Sunan wannan Jam’iyya GPN ta kasa

– Manjo Al-Mustapha yace GPN ce sirrin kasar nan

Dogarin Marigayi Abacha ya kafa sabuwar Jam’iyya

CSO ga Marigayi Abacha Manjo Al Mustafa

Legit.ng na da labari cewa Dogarin tsohon shugaban kasa Marigayi Janar Sani Abacha ya kafa sabuwar Jam’iyya mai suna Green Party of Nigeria watau GPN. Tsohon Dogarin shugaban kasar yace Jam’iyyar GPN ce mafita a Najeriya.

Manjo Hamzah Al-Mustapha mai ritaya yake cewa sabuwar Jam’iyyar ta su watau GPN ita ce mafita a kasar nan kuma mafitar ita ce Jam’iyyar GPN. Al-Mustafa ya bada lagon Jam’iyyar mai launin kore.

KU KARANTA: Kasar Rasha ta ba Najeriya kyautar jirage

Dogarin Marigayi Abacha ya kafa sabuwar Jam’iyya

Dogarin Marigayi Abacha

Shekaru 4 da su ka wuce ne dai aka saki Manjo Al-Mustafa daga gidan yari bayan ya dauki shekaru da dama a garkame inda ake zargin da laifin kashe mai dakin marigayi Abiola watau Kudirat Abiola. A lokacin yace bai da niyyar shiga siyasa.

A jiya ne kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Mr. Babachir David Lawal bisa zargin bada kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba a kwanakin baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tattalin arziki: Ya ake ciki a Najeriya karkashin Buhari

Source: Legit

Mailfire view pixel