Nigerian news All categories All tags
Farawa da iyawa, shugaban NIA da aka dakatar ya fashe da kuka yayinda aka hana shi shiga Aso Rock

Farawa da iyawa, shugaban NIA da aka dakatar ya fashe da kuka yayinda aka hana shi shiga Aso Rock

- Dirakatan hukumar leken asirin Najeriya, Ayodele Oke, ya fashe da kuka yayinda aka hana shi ganawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

- Jim kadan bayan alnta dakatad da shi, jami’an tsaro sun hanashi shiga Aso Villa

-Shugaba Buhari ya baa umurnin bincike mai zurfi cikin zancen kudin da aka gano a Ikoyi da NIA tace mallakarta ce

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Dirakatan hukumar leken asirin Najeriya, Ayodele Oke, ya fashe da kuka yayinda aka hana shi shiga fadar shugaban kasa, Abuja.

Shugaban NIA yayi kokari ganawa da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ne bayan an alanta dakatad da shi da shugaban kasa yayi.

Farawa da iyawa, shugaban NIA da aka dakatar ya fashe da kuka yayinda aka hana shi shiga Aso Rock

Farawa da iyawa, shugaban NIA da aka dakatar ya fashe da kuka yayinda aka hana shi shiga Aso Rock

Yayinda manema labarai ke wurin kuma ya san zasu tunkaro shi, kawai sai ya arce ta wani kofa daban.

KU KARANTA: Buhari ya soke taron NEC na yau

Diraktan ya face da kuka bayan ganin cewa fa, abin da gaske ne. Game da rahoton jaridar Legit.ng, shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David tare da shugaban NIA, Ayo Oke.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel