Yan siyasar Najeriya ne suka jawo faduwar darajar Naira
- Shuagaban ƙungiyar masu hada hadar canjin kuɗaɗen ƙasar waje a ƙasarnan wato ‘ABCON’ Alhaji Aminu Gwadabe ya bayyana haka a wata tattaunawa da ƴan jaridu a jihar Legas
- Yace irin kuɗaɗen da hukumar EFCC ta gano a Lagos da kuma wurare daban-daban a ƙasarnan ya tabbatar da iƙirarin da ƴan kungiyar suka daɗe sunayi
Gwadabe yace ƙungiyar ta damu matuƙa da abinda yake faruwa,amma ahankali asirin maƙiya takardar ƙuɗi ta Naira sai ƙara tonuwa yake.
Legit.ng dai ta samu labarin cewa duk wani ɗan Najeriya na gari ya gane cewa faɗuwar darajar Naira a bune da yafi ƙarfin masu hada-hadar canjin kuɗaɗe.
“Allah ne kaɗai yasan adadin kuɗaɗen da suke ba a bankuna ba a ƙasarnan,” yace.

Yace abune da baza a yarda dashi ba wani mutum ko wasu mutane su ajiye irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe a cikin gida.
KU KARANTA: Mota ta buge wasu mutane 2 har lahira
A tabakin shugaban ƙungiyar yace ɓoye kuɗi da kuma hasashe kan yadda darajar su zata kasance abune da bashi da riba a yanzu, inda ya shawarci jama’a da su daina yin hakan don ci gaban tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Nan ma dai ra'ayoyin yan kasuwane game da tsadar rayuwa saboda karancin daloli
Asali: Legit.ng