An mayar da wasu shugabannin makarantun sakandire malamai saboda shirya magudin jarabawa

An mayar da wasu shugabannin makarantun sakandire malamai saboda shirya magudin jarabawa

- Kwamishinan Ilimi na jihar Ebonyi Mista John Ekeh ne ya bayyana haka loakcin da yake ganawa da ƴan jaridu a Alhamis, 13 ga watan Afrilu

- Hukuncin ya biyo bayan rahoton da hukumar shirya jarabawar kammala babbar sakandire a yankin Afirika ta yamma WAEC tafitar

- Inda ta samu makarantu 20 da kuma waɗansu jami’ai da hannu wajen shirya maguɗin jarabawa

A tabakin Mista Ekeh shugabannin makarantun gwamnati su biyar da aka samu da laifi an rage musu muƙami sannan kuma sauran malamai 25 da kuma jami’an kula da jarrabawa za’a biya su rabin albashinsu na tsawon watanni uku.

Legit.ng ta samu labarin cewa Makarantu 15 waɗanda ba na gwamnati ba da rahoton ya samu da laifi baza abarsu su gudanar da jarrabawar ba a wannan shekara.

Sannan zasu biya gwamnati tarar naira dubu ɗari domin hakan ya zama izina ga sauran makarantu.

An mayar da wasu shugabannin makarantun sakandire malamai saboda shirya magudin jarabawa
An mayar da wasu shugabannin makarantun sakandire malamai saboda shirya magudin jarabawa

Yayi nuni da cewa makarantu biyar da rahoton ya samu da laifi na gwamnati ne, 15 kuma makarantu ne masu zaman kansu.

KU KARANTA: Ku kalli wata coci da ake shan giya don ftar da shedanu

Mr Ekeh shugabannin makarantun biyar da aka samu da laifi an rage musu matsayi zuwa malamai masu koyarwa a aji.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wata makaranta da macizai suka zagaye a Legas

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel