Assha! Naira ta sha kasa a kasuwannin canji (Sabon farashi)
- Darajar Naira a kasuwannin bayan fage ta kara faduwa ya zuwa N410 akan kowace dala daya a jiya
- Babban bankin Najeriya ya dan dakata da zuba daloli a kasuwar canjin.
Ya zuwa yanzu dai labaran da muke samu na nuni ne da cewa darajar ta naira ta fadi a dukkanin kasuwannin ciki hadda ta bayan fage da kuma bankuna.
An samu labarin cewa kuma yanzu haka dai an samu canji na shugabanni a tsakanin yan canjin inda kuma suka tabbatar wa da babban bankin na Najeriya cewa zasu ci gaba da bashi dukkanin cikakken goyon baya dari-bisa-dari.
A yanzu, tattalin arziki yana samu ciwon kai da ciwon ciki.
KU KARANTA: Nayi bakin ciki da ba'a gina alkaryar 'fim' a Kano ba

A jiya ma dai mun ruwaito cewa a ci gaba da kokarin da yakeyi don ganin farashin dala ya ci gaba da sauka, babban bankin Najeriya Central Bank of Nigeria (CBN) karkashin jagorancin Godwin Emefile ya kara malalo $418 miliyan a kasuwannin canji a ranar juma'ar da ta gabata.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyon rayuwar mutane
Asali: Legit.ng