Sojojin Najeriya sun karyata zargin kisan fulani 17 a arewa

Sojojin Najeriya sun karyata zargin kisan fulani 17 a arewa

- Mataimakin Darektan hudda da jama’a na sojin Najeriya Kingsley Umoh ya musanta zargin da wasu kafofin yada labarai suka yi akan su cewa wai sun kashe makiyaya 17 a kudancin jihar Kaduna.

- Ya fadi hakan ne a Kaduna inda ya yi bayanin cewa babu gaskiya a zargin.

Umoh yace gwamnati ta turo su ne domin samar da zaman lafiya a yankin kuma a duk tsawon zamansu sun sami hadin kai da kyakkyawar mu’amula da sarakuna yankin, kungiyar Miyetti Allah da kuma masu fada aji a yankin.

Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya

Legit.ng dai ta samu labarin cewa Ya kuma shawarci mutane musamman masu fada aji a yankin da shugaban al’umman da su kwabi mutane akan yada jita-jita domin hakan hakan zai dagula nasarar samar da tsaro da aka samu zuwa yanzu a yankin.

KU KARANTA: An kara samun wani dan majalisa da takardun boge

Ya ce a ranakun 19 zuwa 22 na watan Maris din da muke ciki rundunar sojin ta sami nasaran kama wasu ‘yan ta’adda guda 4 sannan sun kashe 2 kuma akwai wasu biyu da suke daure a hannun jami’an tsaro.

Daga karshe ya ce sojojin sun ci gaba da aikin duba gari dare da rana a hanya da kewayen Gidan-Waya-Jagindi da Asso.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel