Najeriya ta sha da kyar a hannun Sanagal

Najeriya ta sha da kyar a hannun Sanagal

– Kasar Najeriya ta sha da kyar a hannun Sanagal

– Najeriya ta buga kunnen doki da kasar Sanagal

– Dan wasa Iheanacho ya fitar da kasar daga kunya

Najeriya ta sha da kyar a hannun Sanagal
Najeriya ta sha da kyar a hannun Sanagal

A wani wasa da aka buga jiya da dare Kasar Najeriya ta sha da kyar a hannun takwarar ta Sanagal. Najeriya ta buga kunnen doki da kasar Sanagal inda aka tashi ci 1-1. Matashin Dan wasan nan Iheanacho ya fitar da kasar daga kunya.

Sai daf da tashi sannan dan wasan gaban nan na Man City Iheanacho ya jefawa kasar kwallo inda aka yi canjaras ta bugun finariti na daga kai sai mai tsaron gida. Tauraruwar Dan wasan dai na cigaba da haskawa inda ya jefa kwallaye kusan 5 cikin wasanni 6.

KU KARANTA: An yi wani babban rashi a Najeriya

Najeriya ta sha da kyar a hannun Sanagal
Dan wasan gaban nan na Man City Iheanacho

Najeriya dai ta take wasan ne ba tare da wasu manyan ‘yan wasan ta irin su John Mikel Obi, Victor Moses da Carl Ikeme ba. Nan gaba Najeriya za ta kara fafatawa da kasar Burkina Faso a Filin wasan na Hive da ke Landan

A Ingilar kuma sai makon jiya ne Kungiyar Man Utd ta tashi daga mataki na 6 wanda ta dade a kai. Yanzu haka Man Utd ta dawo mataki na 5 inda ta kerewa Kungiyar Arsenal. Man Utd dai tayi nasara ne bayan ta doke Kungiyar M/Boro da ci 3-1.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel