Kaakakin majalisa da ýan majalisu guda 5 sun yi murabus daga kujerunsu

Kaakakin majalisa da ýan majalisu guda 5 sun yi murabus daga kujerunsu

Kaakakin majalisar dokokin jihar Ondo Jumoke Akindele tayi murabus daga matsayinta, sakamakon rashin jituwa da ake samun a majalisar tun bayan rantsar da sabon gwamna Rotimi Akeredolu.

Kaakakin majalisa da yan majalisu guda 5 sun yi murabus daga kujerunsu

Tsohuwar Kaakakin majalisa

Kaakakin tayi murabus ne a ranar Litinin 20 ga wata Maris tare da wasu yan majalisu guda ciki har da mataimakin Kaakakin Olotu Fatai, shugaban masu rinjaye, mataimakin shugaban masu rinjaye, bulaliyar majalisa da kuma sakataren majalisa.

KU KARANTA: Yansanda sun kama wani boka daya siya karamin yaro a N500, ya kashe shi a harkar tsafi

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito tuni aka nada Mista Malachi Coker a matsayin mukaddashin Kaakakin majalisa.

Kaakakin majalisa da yan majalisu guda 5 sun yi murabus daga kujerunsu

Kaakakin majalisa da yan majalisu guda 5 sun yi murabus daga kujerunsu

Sa’annan yan majalisun sun amince da nadin Olamide George a matsayin shugaban masu rinjaye, sai Mukaila Musa shugaban marasa rinjaye. Wadanda aka nada zasu cigaba da rikon kwarya zuwa ranar da za’a yi sabon zaben shuwagabannin majalisar.

Sai dai wasu rahotannin sun bayyana cewar Kaakakin majalisar tayi murabus ne bayan ta cire wasu makudan kudade da suka kai N15m daga asusun ajiyan kudin majalisar ba tare da sanin shuwagabannin majalisar ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel