Rundunar yan sanda ta tarwatsa taron yan shi'a a jihar Kano

Rundunar yan sanda ta tarwatsa taron yan shi'a a jihar Kano

Labaran dake zuwa mana yanzu haka suna nuni da cewa rundunar yan sandan Najeriya ta tarwatsa taron almajiran Zakzaky a garin Kano a ranar Asabar din da ta gabata.

Rundunar yan sanda ta tarwatsa taron yan shi'a a jihar Kano

Rundunar yan sanda ta tarwatsa taron yan shi'a a jihar Kano

Mun samu wannan labarin ne ta wata sanarwa da kakakin kungiyar yan shi'ar mabiya Ibrahim Zakzaky watau The Islamic Movement in Nigeria (IMN) Ibrahim Musa ya fita tare kuma da rabawa manema labarai.

KU KARANTA: Muhimman shawarwari 7 da Elrufa'i ya ba Buhari

Mai magana da yawun kungiyar yace yan shi'ar sun taru ne domin nuna farincikin su da kuma murna dangane da zagayowar ranar da aka haifi Nana Fadimatu diyar Manzon Allah SAW.

A wani labarin kuma, Hukamar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta kama mutum 34,499 kan laifukan da suka danganci tu'ammali da miyagun kwayoyi a jihohi 36 da kuma babban birnin kasar daga tsakanin shekarar 2012 zuwa 2015.

A wani rahoto da ta fitar, NDLEA ta ce jihar Kano da ke Arewa maso Yamamcin kasar ce kan gaba wajen yawan masu amfani da kwayoyin da ke sa maye, sai jihar Katsina ta biyu, sai jihar Filato ta uku da kuma jihar Ekiti ta hudu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel