Bayan Elrufa'i ya caccaki Buhari, sabon rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC

Bayan Elrufa'i ya caccaki Buhari, sabon rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC

Fitaccen dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar APC, Sanata Rufai Sani Hanga, ya yi tir da yadda Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke kokarin jefa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma Madugun Jam'iyyar APC, Alhaji Atiku Abubakar, a cikin rikicin siyasar jihar Kano.

Bayan Elrufa'i ya caccaki Buhari, sabon rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC

Bayan Elrufa'i ya caccaki Buhari, sabon rikici ya sake barkewa a jam'iyyar APC

Sanata Hanga ya yi wannan suka ne a karshen makon nan dangane da wasu kalamai da suka fito daga bakin Kwankwaso cewa, Atiku, Gwamnan Kano Ganduje tare da gungun wasu mutane na kulle-kullen kafa sabuwar jam'iyya domin tunkarar zaben 2019.

Ya kara da cewa Kwankwaso na sane da cewa Atiku da Ganduje duk 'yan Jam'iyya daya ne, kuma ba su gaba ko tankiya da kowa. Don haka malaman na Kwankwaso kad-da-kanzon-kurege ne kawai ba wani abu ba.

KU KARANTA: Darajar Naira zata kara dagawa - CBN

Don haka ne Hanga ya ce ya kamata Kwankwaso ya ja girman sa, ya daina kitsa zancen da ba gaskiya ba, zuki-ta-Malle da jita-jita domin bata sunan wani, musamman Atiku Abubakar wanda kowa ya san ya na a sahun gaba na kashin-bayan kafa jam'iyyar APC.

Ya ci gaba da cewa ko sau daya Atiku bai taba zama da Ganduje da ma wani ba, domin a yi taron sirrin shirin ficewa daga APC ko kafa wata sabuwar jam'iyya da shi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel