Nigerian news All categories All tags
Kin tantance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Kin tantance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

A ranan Laraba 15 ga watan Maris, majalisan dattawa ta ki tabbatar da Ibrahim Magu saboda wata rahoton da hukumar DSS ta gabatar akanshi.

Amma fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana a ranan Alhamis cewa shugaban kasa ba zaiyi magana akan wannan al’amari ba har sai ya samu wasika daga majalisan dattawa.

A yanzu dai wasu jama’a na nuna hasashe kan cewa tuhumar da ake yi wa wasu daga cikin Sanatoci ne ya hana majalisar amincewa da Magu a matsayin shugaban hukumar ta EFCC.

KU KARANTA KUMA: Fadar shugaban kasa zata maida martani ga majalisa kan kin amincewa da Magu a matsayin shugaban EFCC

Jadawalin wasu daga cikin Sanatocin da ake tuhuma:

1. Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, an tuhume shi da laifin rashin bayyana gaskiya akan kadorin daya mallaka.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Bukola Saraki

2. Sanata Ike Ekweremadu ana tuhumarsa da buga takardar jabu a majalisa.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Ike Ekweremadu

3. Sanata Godswill Apkabio ana tuhumarsa da laifin barnatar da tarin kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 108.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Godswill Apkabio

4. Sanata Buruji Kashamu ana tuhumarsa da laifin sana'ar siyar da muggan kwayoyi, inda yanzu haka ana shari'a akan tisa keyarsa zuwa kasashen turai.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Buruji Kashamu

5. Sanata Ahmad Sani Yarima ana tuhumarsa da laifin barnatar da kudaden masu yawan da suka kai naira biliyan Daya.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Ahmed Sani Yarima

6. Sanata Abdullahi Adamu ana tuhumarsa da laifin barnatar da kudade masu yawan da suka kai naira biliyan 15.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Abdullahi Adamu

7. Sanata Abdulaziz Nyako ana tuhumarsa da laifin barnatar da kudaden masu yawan da suka kai naira bilyan 15.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Abdulaziz Nyako

8. Sanata Joshua Dariye ana tuhumarsa da laifin barnatar da kudaden da suka kai naira bilyan 1.2.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Joshua Dariye

9. Sanata Stella Odua tana kotu inda ake tuhumarta da laifukan cin hanci da rashawa.

Kin tattance Magu: Jadawalin wasu Sanatoci 10 da ake tuhuma

Stella Odua

10. Sanata Sam Egwu ana tuhumarsa da laifin barnatar da kudaden da yawansu yakai naira biliyan 80.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel