Bayanai 10 da zaku sani game da sabon tsarin JAMB, na 7 yana da muhimmanci sosai

Bayanai 10 da zaku sani game da sabon tsarin JAMB, na 7 yana da muhimmanci sosai

- A wannan makon ne hukumar jarabawar shiga jami’a da makarantun gaba da sakandire a Nijeriya wato (JAMB) ta jaddada tabbacin fara sayar da takardun rubuta jarabawar bana, wato shekarar 2017

- Hukumar ta kuma fitar da wasu muhimman bayanai da za su kara wayar da kan daliban da zasu zauna domin rubuta jarabawar a wannan shekara masu matukar amfani

Bayanai 10 da zaku sani game da sabon tsarin JAMB, na 7 yana da muhimmanci sosai
Bayanai 10 da zaku sani game da sabon tsarin JAMB, na 7 yana da muhimmanci sosai

Ga kwararan matakai 10 da kowane dalibi ya kamata a sani kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa:

1. Za a sayar da takardun jarabawar wato (Forms) na tsawon wata guda ne kacal, kuma za a fara sayarwa ranar 20, ga watan Maris, a kammala ranar 19, ga watan Afrilu.

2. Za a sayar da takardun ne a kan kudi Naira 5,500, kuma ya kumshi komai da komai har da kudin rijistar da jadawalin karatu wato (Brochure).

3. Za a rufe rijistar jarabawar ne ranar 22, ga watan Afirilu, 2017.

4. A bangaren dalibai masu bukatar takardun shiga jami’a kai tsaye wato (Direct Entry) kuma, za a fara sayar da nasu daga ranar Lahadi 23, ga watan Afrilu, 2017.

5. Za a zauna jarabawar (JAMB) a ranar 6, da kuma ranar 20, ga watan Yuni, 2017.

Bayanai 10 da zaku sani game da sabon tsarin JAMB, na 7 yana da muhimmanci sosai
Bayanai 10 da zaku sani game da sabon tsarin JAMB, na 7 yana da muhimmanci sosai

6. Ba za a gudanar da jarabawar a ranar 12, ga watan Mayu ba, domin a ba daliban dake jarabawar kammala karatun sakandire, (WAEC) damar rubuta jarabawar Futher Mathematics.

7. Daliban da ke jiran sakamakon jarabawar gaba da sakandire na iya zana jarabawar JAMB, amma su tabbatar suna da sakamakon jarabawarsu a hannu, yayin za a fara bada takardun izinin shiga jami’a.

8. Daliban da suka yi rajistar jarawar JAMB MOCK, za su rubuta jarabawar a ranar 8, ga watan Afrilu.

9. Cibiyoyin CBT, zasu iya cajinkudi har Naira 700, na jarabawar Mock.

10. An samar da sama da cibiyoyi 600 na jarabawar a duk fadin Nijeriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel