Wani ya tona asirin karkatar da abincin 'yan gudun hijira a Bauchi

Wani ya tona asirin karkatar da abincin 'yan gudun hijira a Bauchi

-Asirin inda aka boye kayan abincin 'yan gudun hijira a jihar Bauchi ya tonu sakamakon fallasa hakan da wani ya yi.

-An boye kayayyakin ne da aka karkatar fiye da shekara wanda hakan ya sa wasu suka fara lalalcewa

Wani ya tona asirin karkatar da abincin 'yan gudun hijira a Bauchi
Wani ya tona asirin karkatar da abincin 'yan gudun hijira a Bauchi

Wani mutum a jihar Bauchi ya taimakawa hukumomi bankadao wata ma'ajiya da ake zargin kayyakin abincin 'yan gudun hijira ne da aka karkatar.

An ce kayayyakin abincin na ajiye a ma'ajiyar fiye da shekara, wanda ya jawo lalacewar wasu daga ciki.

Tuni 'yan Najeriya suka soma bayyana ra'ayinsu dangane da wanna lamari mai ban takaici, a shafukan sada zumunta da muhawara kamara haka;

"Wannan wani babban cikas ne ga kokarin gwamnatin tarayya na sake tattara 'yan gudun hijirar, bugu da kari hakan wani zagon kasa ne a fili karara tare da rashin imani."

Wani kuma a na sa ra'ayin "Ba kawai gwamnatocin jihohi da ta tarayya ne ya kamata su dauki nauyin 'yan gudun hijira ba. Nauyi ne na al'umma da ya kamata kowane dan Najeriya ya dauka".

Wani kuma maisuna Maiwada Danmallam cewa ya ke "Za mu iya bayar da gudunmawarmu wajen inganta rayuwar wadannan mutane ko da kuwa ba da kudi ba, a kalla ta wajen sa ido don hana marasa kishi dakile kokarin gwamnati na kyautatawa 'yan gudun hijira."

Ana tsammanin wadanda su ka aikata laifin su tsere don gujewa abin kunya. Sannan an yi kira na musamman ga wadanda ke jihar Bauchi da su tabbatar ba a lalata kokarin gwamnatin tarayya ba.

Masu bayyana ra'ayin na cigaba da cewa, "hakki ne a wayanmu mu sanya idanu don mu tabbatar an dauki matakin da ya kamata don rarrabe aya da tsakuwa tsakanin wadanda su ka aikata laifin da wadanda ba su aikata ba, sannan kuma a tabbatar 'yan gudun hijirar su na samun kulawa yadda ya kamata,"

Har yanzu hukumomin jihar ba su ce komai ba dangane da faruwar lamarin ba

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel