EFCC ta cafke yaron Jonathan bisa badakalar Naira biliyan 2

EFCC ta cafke yaron Jonathan bisa badakalar Naira biliyan 2

-Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa, EFCC ta cafke George Turner, wani abokin siyasa kuma yaro ga tsohon shugaba Goodluck Jonathan, bisa zargin cin hanci da rashawa ranar Talata 14 ga watan Maris

-Turner na da alaka da wasu takardu da aka samu a gidansa da wasu bayanan banki da ke nuna kwararar kudi sama da Naira biliyan 2 wanda bai kamata a ce ya mallaki wadannan kudade ba.

EFCC ta cafke yaron Jonathan bisa badakalar Naira biliyan 2
EFCC ta cafke yaron Jonathan bisa badakalar Naira biliyan 2

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa EFCC ta cafke George Turner, wani abokin siyasa kuma yaro ga tsohon shugaba Goodluck Jonathan, bisa zargin cin hanci da rashawa ranar Talata 14 ga watan Maris na shekarar 2017.

A cewar jaridar Vanguard, kamen na Turner ya zo ne bayan da wani rahoto da ya zarge shi da yin karkatar da Naira biliyan 2, da ake zargin an karkatar da ita daga asusun hukumar ci gaban yankin Niger Delta (NDDC) a tsakanin shekarun 2012 da 2015.

Jami'in yada labarai da hulda da jama'a na hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka.

Uwujaren ya ce, kama Turner na da alaka da wasu takardu da aka samu a gidansa da wasu bayanan banki da ke nuna kwararar kudi sama da Naira biliyan 2 wanda bai kamata a ce ya mallaki wadannan kudade ba.

Ya kuma ce: "An kama Turner a Fatakwal jihar Rivers bisa zargin mallakar kudi Naira biliyan 2, wadanda ake zargin an karkatar da su ne daga hukumar ci gaban yankin Niger Delta NDDC lokacin da ya ke aiki a matsayin mai bada shawara a hukumar".

"Binciken farko da EFCC ta yi, ya tono ajiyar kudi da aka yi a asusunsa na ajiya da na kamfani har Naira biliyan 2".

"A binciken da aka gudanar a gidajensa a Fatakwal da Yenagowa an gano wasu muhimman takardu".

"Turner ya bada muhimman bayanai ga EFCC kuma za a mika shi gaban kuliya da zarar an kammala bincike."

Tsohon shugaban kasa Godluck Jonathan ne ya kafa hukumar ci gaban yankin Naija Delta a lokacin yana mulki.

Sai kamar yadda wasu ke zargi, a maikamakon hukumar ta yi aikin da doka ta kafata sai kudaden suka yi batar dabo.

Ga wani hoton bidiyo kan ra'ayin jama'a

Asali: Legit.ng

Online view pixel