An hana jigila daga Kaduna zuwa Abuja a jirgi mai saukar ungulu

An hana jigila daga Kaduna zuwa Abuja a jirgi mai saukar ungulu

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaron, Babagana Munguno ya hana shirin da ake yi na yin jigila daga Kaduna zuwa Abuja a jirgi mai saukar ungulu, biyo bayan rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja

Wani kamfanin mai suna Marple Aviation Logistics Limited da ke jigilar jirgin sama mai saukar ungulu, ya tallata shirinsa na jigilar matafiya daga filin jirgin saman Kaduna zuwa filin wasan kwallon kafa na Abuja a kan kudi naira 49,999.

Sakamakon rufe filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a Abuja domin gudanar da wasu gyare-gyare da zai dau tsawon wani lokaci

Amma wata wasika mai taken "Hana jigilar jirgi mai saukar ungulu a birnin Abuja" daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaron, ta umarci fasinjoji da suka sauka a jiragen sama zuwa Kaduna da cewa su bi ta mota ko ta jirgin kasa zuwa Abuja.

Wasikar mai kwanan wata 6/3/2017 wacce jaridar Daily Nigerian ta yi ido hudu da ita ta ce:

"A sakamakon rufe filin jirgin sama, matafiya za su dinga tafiya a mota ko a jirgin kasa daga filin jirgin sama na Kaduna zuwa Abuja".

Babu tantama wannan zai kawo cikas ga zirga-zirgar matafiya wadanda za su so yi amfani da jirgi mai saukar ungulu don saukin tafiya da kuma tsaro.

Sanarwa ta kuma ci gaba da cewa, "Ku sani cewa ana lura da sararin samaniyar birnin Abuja kuma jami'an tsaro ne kadai ko wadanda su ka samu izini daga fadar shugaban kasa ke iya tashi saboda dalilai na tsaro".

"Saboda haka, ku sani cewa babu wani jirgi mai saukar ungulu da zai tashi a sararin samaniyar Abuja."

A ranar 9 ga watan Maris ne aka karkatar da jiragen da ke tashi da sauka a Abuja zuwa filin na Kaduna, wanda tafiyar sa'a 2 ce a mota.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne kadai yayi amfani da jirgi mai saukar ungulu daga Kaduna zuwa Abuja a lokacin da ya dawo daga Landan bayan hutun da ya yi na karbar magani.

Ga wani hoton bidiyo kan batun rufe filin jirgin saman Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel