'Yan gudun hijirar Najeriya 22,463 sun dawo daga jamhuriyar Nijar

'Yan gudun hijirar Najeriya 22,463 sun dawo daga jamhuriyar Nijar

-Kimanin 'yan gudun hijira 22,463 da suka tsere daga Najeriya daga zuwa Jamhuriyar Nijar ne suka dawo gida a 'yan kwanakin nan

-'Yan gudun hijrar wadanda yawacinsu daga jihar Borno ne, sun tsere ne a sakamakon rikicin Boko Haram wanda ya raba su da muhallinsu

'Yan gudun hijirar Najeriya 22,463 sun dawo daga jamhuriyar Nijar
'Yan gudun hijirar Najeriya 22,463 sun dawo daga jamhuriyar Nijar

Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA da takwararta ta jihar Borno BOSEMA, da kuma hadin gwiwar hukumar shige da fice ta Najeriya, sun yi rijista ga 'Yan gudun hijira da su ka dawo daga jamhuriyar Nijar zuwa garin Damsak a karamar hukumar Mobar ta jihar Borno.

Mai magana da yawun hukumar NEMA na yankin Arewa maso gabas, Abdulkadir Ibrahim ya ce, dawowar 'Yan gudun hijirar ya biyo bayan yarjejeniyar da kasashen Najeriya da Kamaru da Nijar su ka sanyawa hannu don dawo da 'yan gudun hijirar cikin koshin lafiya.

Ana tsammanin wasu sama da 10,000 za su dawo nan da 'yan kwanaki.

Abdulkadir ya kuma ce "Kungiyar kasa da kasa ta Red Cross ta na samar da kayan abinci ga 'yan gudun hijirar yayin da kwamitin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ke samar da magunguna da taimakon jami'an karamar hukumar Moba".

A wani mataki na rigakafi, shirye-shirye sun yi nisa na karbar wasu 'yan gudun hijira da ake tsammanin dawowar su daga Kamaru ta cikin garin Banki da ke karamar hukumar Bama da Ngamboru Ngala da ke karamar hukumar Ngala, cewar wani rahoton Jaridar Daily Nigerian.

Jaridar ta rawaito cewa, wata tawagar masu jin kai da ta hada da ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan jin kai, OCHA, da Kungiyar abinci ta duniya WFP, da ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da 'yan gudun hijira UNHCR, da kuma hukumomin gwamnati za su gudanar da bincike don cike gurbin da ake samu wajen samar da matsuguni da abinci da ruwa da kuma tsaftar muhalli a sansanonin 'yan gudun hijira a jihar.

A karshen shekarar 2016 ne rundunar sojin Najeriya ta samu galaba a kan 'ya ta'adan Boko Haram a inda ta fatattake su daga dajin Sambisa wanda hakan ya karya laggon 'yan kungiyar bayan 'yantar da wurare da yawa da sojin suka yi.

Ga wani hoton bidiyon murnar dawowar shugaba daga jinya a Landan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel