Sauran kiris mu kai ga shugabancin kasar nan - Babbar Akantar jihar Kano

Sauran kiris mu kai ga shugabancin kasar nan - Babbar Akantar jihar Kano

- Mai rike da mukamin babbar akantar jihar Kano Hajiya Aisha Muhammadu Bello ta ce mata na ba da gagarumar gudunmawa wajen gina kasa kuma da sannu matan za su kai ga shugabancin kasar nan

- Hajiya Aisha ta kuma ce nadin Hajiya Amina Mohammed tsohuwar ministar kula da muhalli a matsayin mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya ya daga darajar matan Najeriya da arewa

Sauran kiris mu kai ga shugabancin kasar nan - Babbar Akantar jihar Kano
Sauran kiris mu kai ga shugabancin kasar nan - Babbar Akantar jihar Kano

Mai rike da mukamin babbar akantar jihar Kano Hajiya Aisha Muhammadu Bello ta ce, mata na ba da gagarumar gudunmawa wajen gina kasa, kuma da sannu matan za su kai ga shugabancin kasar nan.

Hajiya Aisha ta kuma ce nadin Hajiya Amina Mohammed tsohuwar ministar kula da muhalli a matsayin mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya ya daga darajar matan Najeriya da arewa.

Hajiya Aisha ta yi wannan bayani ne a wata hira ta musamman da ta yi da jaridar Legit.ng a Kano a ranar 12 ga watan Maris shekara ta 2017.

Aisha Muhammad Bello ta kuma ce, kai wa ga shugabancin kasar nan ga mata ba abu ne na yanzu ba, sai dai sannu a hankali, da kuma lokaci kamar yadda Allah Ya kai ta kan wannan mukami da taimakon gwamnan jihar Kano.

Tsohuwar ministar muhalli Amina Muhammad ta zama mataimakiyar babban sakataren majalisar dinkin duniya, an kuma rantsar da ita, ta kuma kama aiki a farkon wannan wata na Maris na shekarar 2017.

Kafin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada ta babbar akantar jihar, Hajiya Aisha ita ce kwamishiniyar kula da kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar.

Gwamna Ganduje ya kafa tarihi a arewacin kasar nan da nada ta a matsayin Akanta janar ta jihar a shekarar da 2016.

Ga hoton murnar dawowar Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel