An kama mata mai shekaru 57 dauke da hodar iblis a filin jirgin sama na Lagas

An kama mata mai shekaru 57 dauke da hodar iblis a filin jirgin sama na Lagas

- An kama wata mata mai shekaru 57, Omolara Morayo Adeyemi a Filin jirgin sama na Lagos dauke da hodar iblis a akwatin ta

- An rahoto cewa Morayo na hanyar ta na zuwa kasar Saudiyya don aikin umrah lokacin da aka kama ta

An kama wata yar kasuwa mai shekaru 57 da ke siyar da kayayyakin sa wa a kasuwar Balogun a Lagas, Omolara Morayo Odeyemi, dauke da hodar iblis a akwatin ta.

Hukumar dake kula da magunguna ta kasa (NAFDAC) a wata sanarwa da tayi a ranar Asabar, 11 ga watan Maris, tace Odeyemi na a kan hanyar ta na zuwa kasar Saudiyya don aikin umrah lokacin da aka kama ta, Sahara reporters ta ruwaito.

An kama mata mai shekaru 57 dauke da hodar iblis a filin jirgin sama na Lagas

Mitchell Ofoyeju wanda tayi magana a madadin hukumar NAFDAC tace Odayemi ta tanadi dukkan abubuwan da ake bukata don umran a jakar ta sannan sai aka boye holar iblis din a tsakanin sauran abubuwan.

Shugaban hukumar NDLEA a filin jirgin Murtala Muhammed, Lagas, Ahmadu Garba yayi bayaninb cewa an samu dauri biyu na hodar iblis a cikin akwatin ta.

KU KARANTA KUMA: Hausawa sun bar Ile-Ife bayan rikicin kabilanci da yayi sanadiyan mutuwar mutane da dama

Garba ya ce: “An kama wata pasinja mace, Omolara Morayo Odeyemi dake dauke da tikitin kasar Masar daga Lagas zuwa kasar Saudiyya dauke da hodar iblis mai nauyin 1.595kg.

“An gano daurin hodar iblis din dake boye a karkashin jakar ta lokacin da ake tantance pasinjoji zuwa dakin tashi. Sai da muka barka jakar sannan muka gano hodar iblis din saboda yadda aka saka shi cikin tsanaki. A take aka kama ta kuma a yanzu haka ana cikin bincike.”

Da aka tambayi Odeyemi ta bayyana cewa kawarta ce ta sanya ta hanyar safaran miyagun kwayoyi.

Odeyemi ta ce: “Na kasance mai fataucin kayayyakin sa wa a kasuwar Balogun, Lagas, ina da ‘ya’ya biyu sannan na aurar da ‘yata harma tana da ‘ya’ya. Kwanaki, na fada ma kawa ta cewa ina son zuwa sauke farali a wannan shekarar sai tayi alkawarin daukar nauyin tafiya ta.

“A hakan ne ta karbi fasfot dina, ta hada mun duk takardun da ya dace na tafiya sannan ta siya mun tikitin jirgi na kasar Masar. Alfarman da ta bukata daga gare ni shine wai na dauki wani jaka zuwa Sadiyya.

“Ta kuma fada mun cewa wani zai karbi jakar daga hannuna a Jeddah. Jaka ne da babu komai a ciki don haka na zuba kayyayaki na a ciki. Da na isa filin jirgi, jami’ai suka gano hodar iblis a cikin jakar lokacin da suke bincike sannan aka kama ni.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel