Murnar dawowar Buhari: Wani ya yi rabon kilishi Naira 200,000 kyauta don murna

Murnar dawowar Buhari: Wani ya yi rabon kilishi Naira 200,000 kyauta don murna

Wani dan gani kashenin shugaba Buhari a ya yi rabon kilishin na sana 'arsa na kimanin Naira N200,000 kyuata ga jama'a don nuna murnarsa ga dawowar shugaban daga jiyyara da ya ke yi a birnin Ladan

Murnar dawowar Buhari: Wani ya yi rabon kilishi Naira 200,000 kyauta don murna
Murnar dawowar Buhari: Wani ya yi rabon kilishi Naira 200,000 kyauta don murna

Wani dan gani kashenin shugaba Buhari wanda ba a bayyana sunannsa ba mai sana'ar kilishi ya yi rabawa jama'a kilishin na kimanin Naira N200,000 kyauta don nuna murnarsa ga dawowar shugaban daga jiyyar da ya yi a birnin Landan.

Wannan mutumin mai sana'ar sayar da kilishin ya yi hakan ne saboda nuna matukar kaunarsa ga shugaban kasa, an kuma sanya hotunan ne na wannan shagalin cin naman kilishi a wurin sana'ar ta sa a kuma wani wuri da ba a bayyana ba.

Ga dai bikin nan a cikin hotuna kamar yadda shafin intanet na Lailas blog ya bayar da labari.

Murnar dawowar Buhari: Wani ya yi rabon kilishi Naira 200,000 kyauta don murna
Murnar dawowar Buhari: Wani ya yi rabon kilishi Naira 200,000 kyauta don murna

Tun lokacin da labarin shugaba Buhari ya sauka filin rundunar sojin sama na Kaduna a jiya Juma'a ne 10 ga watan Maris shekarar 2017, matasa da sauran al'umma musamman a arewacin kasar a ke ta murna da nuna farin cikin dawowarsa.

An dai sha rade-radin tsananin rahsin lafiyar shugaba Buhari da ta kai wasu na cewa ya mutu, ku kuma ba zai dawo da rai ba.

Ga daya daga cikin hotunan bidiyon murnar dawowar Buhari da aka yi a Daura

Asali: Legit.ng

Online view pixel