Gidan jaridar NAIJ.COM na neman masu aiko da rahotanni da za su shiga wani sabon shirin na aiko da rahotanni daga inda suke

Gidan jaridar NAIJ.COM na neman masu aiko da rahotanni da za su shiga wani sabon shirin na aiko da rahotanni daga inda suke

Gidan jaridar Legit.ng ta yi tsayin daka wajen bayar da labarai da dumi-duminsu, kuma masu matukar muhimmanci ga miliyoyin ‘yan Najeriya.

La’akari da cewa karar mu ya kai tsaiko wajen bayar da labarai da kuma wasu muhimman al’amuran da ke faruwa a manyan garuruwan Legas da Abuja, da kuma ganin cewa wasu labaran daga sauran lungu da sako na wasu yankun nan kasar nan ka iya wuce mu, da sauran wasu kafofin yada labarai na kasa. Hakan ta sa ma muka fito da wanin sabon shiri na aikowa da rahotani daga inda ka ke.

Shin yaya shirin ya ke?

An tsara shirin aiko da rahotanni daga in da ka ke ne, domin jan hankalin musu burin shiga aikin jarida

Da kuma aiko da rahotanni daga wadanda za su iya kasancewa mazauna a ko ina ne a Najeriya, in ban da garuruwan Abuja da Legas a inda muke da ofisoshi.

Takamaimai mu na sha’awar rahotanni ne a kan

  • Muhimman al’amuran da ke faruwa a inda ka ke
  • Manya-manyan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa da kuma tasirinsu a kan jama’ar wurin da ka ke.
  • Duk wani labarin da sauran kafofin yada labarai ba su iya bayar da shi ba.

Abubuwan da ake bukata na shiga shirin

  • Dole ne ya kasance ka na da abubuwan da ka taba wallafawa (ciki har da shafukan Intanet)
  • Dole ne ya kasance ka na da masaniyar irin abubuwan da ke faruwa a inda ka ke, gami da sha’war bayar da labarinsu ga jama’ar kasa baki daya.
  • Kasancewar ka sani ko iya fasahar zamani ta hakar yada labarai watau digital media, na da kyau, sai dai ba lallai ba ne.

Ta yaya za a yi aikin?

Da farko, aikin na wucin gadi ne, kuma wata babbar dama ce ta yin aiki da daya daga cikin gidajen jaridu na intanet da suka yi fice a kasar nan. Daga daga karshe ka zama cikakken ma’aikaci.

Ta yaya zan shiga shirin?

Babu wahala, kawai shiga nan domin cike takardar shiga shirin. Mu kuma za mu neme ka.

Bugu da kari

Muna neman masu shafuka a intanet watau websites, da kuma masu shafuka na kashin kansu watau blogs wadanda za mu hada hannu da su, mu rika musayar bayanai cikin kyakkyawar fahimta da amfanar juna.

Idan kana da shafi a intanet wanda kuma ka ke wallafa bayanai na cikin gida a kai – a kai, aiko mana da wasika ta wannan adireshi; blogger@corp.legit.ng da taken; shirin aika rahotanni a inda ka ke a saman wasikar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel