Dokar kayyade aure ta Allah ce ba sarkin Kano Ba - Shugaban Izala

Dokar kayyade aure ta Allah ce ba sarkin Kano Ba - Shugaban Izala

A cikin wata tattaunawa da majiyar mu, Shugaban kungiyar Izalatul Bid’a wa ikamatus sunnah na kasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana muhimmanci hadin kai tsakanin musulmi, amma ya ce su a Izala ba za su taba hada kai da masu zagin sahabban Annabi da matansa ba.

Dokar kayyade aure ta Allah ce ba sarkin Kano Ba - Shugaban Izala
Dokar kayyade aure ta Allah ce ba sarkin Kano Ba - Shugaban Izala

Sannan Malamin ya kuma bayyana rashin lafiyar Shugaba Buhari da cewa jarabawa ce. Don haka ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da yi masa addu’ar Allah ya bashi lafiya. Sannan ya kuma bayyana dokar da ake shirin kafawa a Kano da cewa dokar Allah ce, ba wai ta Sarkin Kano ba.

Lokacin da aka tambaye shi game da shirin da mai Martaba Sarkin Kano yake yi na ganin an kafa dokokin aure a jihar kuwa, sai ya kada baki yace:

"Gaskiya wannan doka ba ta Sarkin Kano ba ce, dokar Allah ce. Domin Allah ya fada mana a cikin Littafinsa cewa idan za ku yi aure ku auri mata biyu ko uku ko hudu. Amma idan ba za ku iya yin adalci ba, to ku auri daya. Saboda haka wannan abu yana nan. An kawo bidi’o’i ne daga baya duk aka zuba a harkar aure.

"Kuma na hadu da mai martaba Sarkin Kano ya shaida min cewa suna gayyatarmu Malamai da a zo a duba wannan kundi da suka yi, idan akwai wani abu da ya saba a cire. Idan kuma akwai abin da ba a sa ba, to a sanya shi."

Ya ce, idan Malamai sun gama dukkan gyaran da ya kamata a yi, sai a mika wa Majalisar Dokokin jihar, domin ta amince da shi ya zama doka. Saboda haka muna goyon bayan dokar Allah.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel