Yan zuga ne suka shiga tsakanina da Kwankwaso - Ganduje

Yan zuga ne suka shiga tsakanina da Kwankwaso - Ganduje

Masu sa ido a siyasar Kano da ke Najeriya sun bayyana cewar, rashin jituwar da ta fito fili tsakanin Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje da tsohon mai gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na yi wa jihar tarnaki wajen ci gaban da aka dauko.

Yan zuga ne suka shiga tsakanina da Kwankwaso - Ganduje
Yan zuga ne suka shiga tsakanina da Kwankwaso - Ganduje

Sai dai Gwamna Ganduje ya ce a shirye yake ya sasanta da Sanata Kwankwaso don ganin an dinke barakar da ke tsakaninsu.

A zantawarsa da majiyar mu, Gwamnan ya ce, akwai ‘yan ziga a rashin jituwar da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan na Kano.

KU KARANTA: Darajar Naira ta fadi bayan dawowar Buhari

A wani labarin kuma, Labaran da ke shigo mana yanzu suna nuni da cewa darajar Naira ta sake faduwa a yau din nan Juma'a 10 ga watan Maris awowi kadan bayan dawowar shugaba Buhi daga Landan.

Rahotannin da muka samu daga kasuwannin canji na cikin gida na nuni da cewa a yau din darajar Naira ta fadi zuwa N463 a kan kowace dala a maimakon N462 da aka saida ta a jiya Alhamis 9 ga wata.

Haka zalika an saida kudin Pounds na kasar Birtaniya a kan N555 mai makon N550 da aka saida shi kafin dawowar shugaban.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel