Rashin wutan lantarki: Fashola ya bar aiki ko ya yi gyara nan da kwana 30 – Inji wani kungiya

Rashin wutan lantarki: Fashola ya bar aiki ko ya yi gyara nan da kwana 30 – Inji wani kungiya

- Rashin wutan ya fi wahala a ta Kudancin Najeriya. Domin haka, Fashola ya gaza kan aiki da ya karba

- Fashola ya kasa samun nasara akan ya kara karfin wuta daga 4,320 da ya same shi har yau

- Acikin kwana 30 da kungiyar ta ba minista Fashola, ana nema ya san abin yi akan kudin wuta da ana yanke ma mutane da bai yi daidai ba

- Sun ce idan Fashola ba zai iya duk wannan ba, ya bar kashi na wuta a duk aiki da aka mika mishi ko ya rubuta takarda na barin aiki

Rashin wutan lantarki: Fashola ya bar aiki ko ya yi gyara nan da kwana 30 – Inji wani kungiya
Rashin wutan lantarki: Fashola ya bar aiki ko ya yi gyara nan da kwana 30 – Inji wani kungiya

Da damuwar rashin wutan lantarki na ta tafiya a kasar, wani kungiyar goyon bayan dimukraɗiya sun ba Babatunde Fashola, umarni kan ya bar aiki nan da kwana 30 ko kuma ya san yadda zai yi a fara samun wuta kan lokaci.

Mai maganan kungiyar Dede Uzor A. Uzor ya yi wannan magana ne a takarda da kungiyan ya fito da ma yan labari. Ya ce rashin wutan ya fi wahala a ta Kudancin Najeriya. Domin haka, Fashola ya gaza kan aiki da ya karba.

KU KARANTA: Ba’a nada ni shugaban Kastam domin in sa Inifam ba – Hameed Ali ga Majalisan dattawa

Inji Uzor, wai Fashola ya kasa samun nasara akan ya kara karfin wuta daga 4,320 da ya same shi har yau. Akan wanna ne y ace Fashola ya gaza kan aiki da aka bashi. Ya ce: “Maimako ya karu daga 4,320, ya ragu ne zuwa 1,000. Wannan al’amari yasa duk kasar ta rasa wuta a watan Janairu kwana 30 da ko ina ya koma duhu domin mun shiga megawatt 0.”

KU KARANTA: YANZU-YANZU! Darajar Naira ta sake faduwa bayan dawowar Buhari

Acikin kwana 30 da kungiyar ta ba minista Fashola, ana nema ya san abin yi akan kudin wuta da ana yanke ma mutane da bai yi daidai ba. Takardan ta kara fada: “Muna neman a raba wa kowa a Najeriya akwatin mai nuna lamba wuta da aka amfani da wato ‘prepaid meter’."

Sun ce idan Fashola ba zai iya duk wannan ba, ya bar kashi na wuta a duk aiki da aka mika mishi ko ya rubuta takarda na barin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel