YANZU-YANZU: Tawagar motocin gwamna shettima sun yi hatsari, wani babban jami’insa ya mutu

YANZU-YANZU: Tawagar motocin gwamna shettima sun yi hatsari, wani babban jami’insa ya mutu

Wata mumunar hatsari ya faru da tawagar motocin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Juma'a, 10 ga watan Maris yayin da hatsarin ya yi sanadiyar rasuwar babban jami'in na musamman ga gwamnan kan yarjejeniya malam Farouk Farouk.

YANZU-YANZU: Tawagar motocin gwamna shettima sun yi hatsari, wani babban jami’insa ya mutu
Tawagar motocin gwamna shettima sun yi hatsari, wani babban jami’insa ya mutu

Wani direba kuma ya ji rauni a hatsarin, amma an kai sa asibiti don yi masa jinya.

Jaridar Cable ta ruwaito cewa hatsarin ta faru a hanyan babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Ba tabbas ko Shettima na kan hanyarsa zuwa yin maraba wa Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya dawo kasar bayan hutun duba lafiyarsa a Landan.

Shettima ba ya cikin gwamnonin da suke tare da shugaba Buhari a Abuja fadan shugaban kasa bayan dawowarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel