Sojoji sun kama mutumin dake yi ma Boko Haram leƙen asiri yayin da suke kakkaɓe ýan ta’adda daga ƙauyukan Borno

Sojoji sun kama mutumin dake yi ma Boko Haram leƙen asiri yayin da suke kakkaɓe ýan ta’adda daga ƙauyukan Borno

A cigaba da kokarinsu na kakkabe yan ta’addan Boko Haram dake tserewa daga dajin Sambisa, rundunar soji ta OPERATION LAFIYA DOLE dana OPERATION HARBIN KUNAMA II sun kara kaimi a ayyukansu.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno
mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri, Alhassan Garba

Kaakakin watsa labarai na rundunar sojan kasa Birgediya Sani Kukasheka Usman ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 9 ga watan Maris inda yace: “Dakarun runduna ta 232 sun gudanar da sintiri a kauyukan Muchalla, Lade da Bodeno sun don tabbatar da yayan Boko Haram basu sake komawa kauyukan ba. Haka zalika sun gudanar da wani sintirin a kauyen Garkida har zuwa Dzangwalla inda suka hallaka wasu yan Boko Haram da suka tsere daga dajin Sambisa.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno
Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

“Su kuwa dakarun runduna ta 23 sun gudanar da nasu sintirin ne a kauyen Kolkol don tabbatar da sun mamaye yankin tare da hana yan ta’addan boyewa a cikin kauyen saboda kusancinsa da iyakar kasar Kamaru. Suma dakarun da aka jibge a sansanin sojoji dake garin Hong sun tattare hanyoyin da suka nufi kauyukan Mararrabar Pella, Kalaa da Shangui don cimma duk wani dan Boko Haram daya biyo wannan hanyar.”

KU KARANTA: Dan Najeriya ya hallaka kansa bayan faɗowa daga gidan sama mai hawa 31

Usman yace dakarun sojan runduna ta 27 kasa sun cafke Alhassan Garba, mutumin dake tattara ma Boko Haram bayanan sirri, tare da yi musu leken asiri.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno
Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

Yace: “Bayan samun bayanan sirri daga wasu yan kishin kasa, Dakarun runduna ta 27 sun smau nasarar cafke mutumin dake tattara ma Boko Haram bayanan sirri, tare da yi musu liken asiri, mai suna Alhassan Garba a kauyen Azare dake karamar hukumar Gujba na jihar Yobe.

“Bincike ya nuna cewar diyar Alhassan, Lami ALhassan Garba na auren wani kasurgumin dan Boko Haram mai suna Musa Isah, wanda ya tsere daga kauyen zuwa jihar Kano, kuma min bi shi hark anon, mun kama shi, a yanzu dukkaninsu suna hannu ana gudanar da bincike akan su.''

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno
Dan Boko Haram, surukin Alhassan Garba

Usman ya cigaba da fadin: “Dakarun runduna ta 233 tare da hadin gwiwar rundunar hadaka ta 29 da dakarun runduna ta 212 sun gudanar da aikin kakkabe yan ta’adda a kauyen Lawanti. Kazalika dakarun rundunar hadaka ta 154, da na 29 sun gudanar da sintiri cikin shirin ko-ta-kwana akan hanyar Mauli da Alagarno don mamaye yankin daga hana yan Boko Haram samun wurin buya.

“Dakarun sun sake yin wani sintiri akan hanyoyin kauyukan Sansan da Bulabulin shima don hana ma yan Boko Haram sakat. Suma dakarun rundunar hadaka ta 156 tana gudanar da nata sintirin a yankin Ngula-Jayiwa da Kukuram-Abalam don hana ma yan Boko Haram mabuya.

Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno
Sojoji sun kama mutumin da keyi ma Boko Haram leken asiri yayin da suke kakkabe yan ta’adda daga kauyukan Borno

“Dakaru runduna daban daban suna gudanar da sintiri na musamman a yankunan Lame, Bingel, Gumau, Toro, Panshanu, Tashan Kaji and Tashan Durumi. Others include Sabon Gari, Yelwan Duguri, Darazo, Soro, Wailo, Drum, Bukutumbe, Dogon Ruwa, Dingis, Dabar Bagam Gomo, da sauransu. Haka zalika dakarun na gudanar da aikin HARBIN KUNAMA na II a dazukan Bauchi da Gombe, kuma ana samun nasara gagaruma.

“Suma runduna na 231 da 331 dake jibge a kudancin Borno ba’a barsu a baya ba, inda suke cikin shirin kota kwana sun gudanar da sintiri tare da kai samame a yankunan nasu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel