Kudin da Najeriya ke samu na gas yayi kasa

Kudin da Najeriya ke samu na gas yayi kasa

Kudin da kasar nan take samu ta bangaren man gas ya lula kasa sosai a wani bincike da aka gudanar. NLNG dai ya kan ba Najeriya kaso daga cikin cinikin sa na shekara amma wannan karo ba a samu kudi mai yawa ba.

Kudin da Najeriya ke samu na gas yayi kasa
Kudin da Najeriya ke samu na gas yayi kasa

Kamar yadda muka bayyana kason da Najeriya ta ke samu daga gas ta hannun NLNG yayi kasan da ba a taba jin labarin irin sa ba cikin shekaru 10. Najeriya dai ta samu sama da Dala Biliyan $1 a 2015 a matsayin kason ta na gas sai dai wannan shekarar da ta wuce abin da aka samu Dala Miliyan 365 ne kacal.

Idan aka lura dai Najeriya ta rasa sama da kashi 65 bisa 100 na kason da ta samu shekarar bara. Hakan dai na nuna yadda farashin man ya fadi kenan a kasuwar Duniya da kuma rashin ciniki saboda karancin masu saye.

KU KARANTA: Ba mu fata Buhari ya mutu-PDP

Ana dai sa rai abubuwa za su murmure wannan shekarar bayan da farashin ganga ya fara babbakowa a Duniya. Najeriya dai tana cikin kasashen da su ka fi kowa gas a Duniya, ita ce kuma ta farko a Nahiyar.

Kuma dai yanzu haka ana sa ran isowar wasu jirage har 29 zuwa Najeriya dauke da kayan abinci da kuma mai. Wadannan jirage za su shigo ne ta tashar ruwan kasar da ke Garin Legas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel