UNICEF ta raba ma makarantun jihar Katsina 193, naira miliyan 48.2

UNICEF ta raba ma makarantun jihar Katsina 193, naira miliyan 48.2

Cibiyar kula da yara ta majalisar dinkin duniya, UNICEF ta fitar da kimanin N48.2m ta rabar ga makarantun jihar Katsina su 193 don inganta harkar karatu da koyarwa a makarantun.

Cibiyar UNICEF ta raba ma makarantun jihar Katsina 193, naira miliyan 48.2
Cibiyar UNICEF ta raba ma makarantun jihar Katsina 193, naira miliyan 48.2

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kowanne makaranta ta samu N250,000 duba da tsare tsaren cigaban makarantar.

Da take jawabi yayin bada cek din kudin, shugaban UNICEF a Najeriya Padmavathi Yedla ta jaddada bukatar al’umma dasu sanya hannu wajen kai yara kanana makaranta, musamman yaya mata.

KU KARANTA: Almajiri ya tsinci N615,000, kuma ya mayar ma mai shi, amma ko kasan dalilinsa na mayarwa?

Tace kudaden da aka baiwa makarantun, an basu ne don su gudanar da tsare tsaren cigaban makarantun, inda ake tsammanin sun san matsalolin da makarantun ke fuskanta, kuma sun san hanyoyin magance su.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Katsina Aminu Masari yace suna maraba da irin wannan taimako, kuma gwamnati zata yi iya bakin kokarinta na ganin ta cigaba da samar da yanayi mai kyau a makarantun jihar don inganta ilimi gaba ki daya.

Gwamna Masari ya cigaba da fadin gwamnatinsa na kokarin samar da wata doka da zata hukunta duk iyayen da suka hana yayansu zuwa makaranta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel