Dan Najeriya ya hallaka kansa bayan faɗowa daga gidan sama mai hawa 31

Dan Najeriya ya hallaka kansa bayan faɗowa daga gidan sama mai hawa 31

An tabbatar da mutuwar wani dan Najeriya a kasar Malaysia mai suna Chimaobi daya fado daga gidan sama mai hawa 31, inda ya kashe kansa.

Dan Najeriya ya hallaka kansa bayan faɗowa daga gidan sama mai hawa 31
Dan Najeriya ya hallaka kansa bayan faɗowa daga gidan sama mai hawa 31

Wani ma’abocin kafar sadarwa na Facebook Butibalati Uzodimma ne ya bayyana labarin, inda yace Chimaobi wanda ake yi ma lakabi da suna Paco Jelapa na Malaysia ya wurgo kansa ne daga gidan saman mai hawa 31 tare kwala ihu mai tsanani.

KU KARANTA: Shugaban ƙungiyar ta’addanci ‘Al-Shabab’ ya miƙa wuya ga gwamnatin ƙasar Somalia

An jiyo ihun Chimaobi yana ihu “Ku kyale ni, ku rabu dani” jim kadan kafin mutuwar tasa, sai yayi wurgi da wayarsa da kuma na’urar kwamfuta na tafi da gidanka, daga nan kwatsam sai ya wurgo kansa kasa daga gidan saman.

Ga dai yadda Uzodinma ya bada labarin:

“Ka huta lafiya cikin aminci Jelapa na Malaysia, abokina, dan ajinmu, abokin zaman daki na. na ji shi yana ihun ku rabu dani, daga nan sai yayi wurgi da na’urar kwamfutansa da wayarsa ta taga, nan kuma ya bisu ya fado daga sama. Allah kadai ya san dalili.!

''Da fatan zaka huta ciki aminci! Butibalati na kewarka Chimaobi”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel