Ka yi hakuri ka maida Wazirin ka-Atiku ya roki Sarkin Bauchi

Ka yi hakuri ka maida Wazirin ka-Atiku ya roki Sarkin Bauchi

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya gana da Sarkin Bauchi a Yau dinnan kamar yadda muke samun labari yanzu haka.

Ka yi hakuri ka maida Wazirin ka-Atiku ya roki Sarkin Bauchi
Ka yi hakuri ka maida Wazirin ka-Atiku ya roki Sarkin Bauchi

Atiku Abubakar Turakin Adamawa ya gana da Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwan Sulaiman Adamu a game da matakin da ya dauka na dakatar da Wazirin sa kwanan nan idan ba a manta ba.

A jiya ne muka samu labari cewa Mai martaba Sarki ya tsige Wazirin sa a dalilin rashin biyayya da ake samu. Sai dai Turakin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ya garzaya wurin Sarki inda ya nemi yayi afuwa ga Alhaji Bello Kirfi wanda yake Wazirin Bauchi a da.

KU KARANTA: Za a shigo da abinci Najeriya

Ka yi hakuri ka maida Wazirin ka-Atiku ya roki Sarkin Bauchi
Ka yi hakuri ka maida Wazirin ka-Atiku ya roki Sarkin Bauchi

Atiku Abubakar ya nemi a yafewa Waziri laifin da yayi wa Masarauta domin martabar ta, yace kowa ajizi ne. Sarkin ya nuna godiya ya kuma bayyana cewa zai yi wani abu game da lamarin kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust.

Kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN tayi kuka inda tace har yanzu ana kashe mata Jama’a a boye. CAN tace duk da cewa akwai Jami’an tsaro a Yankin Kudancin Kaduna ana yi mata kisan dauki dai-daya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel